1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton kotun Hage a game da kissan kiyasun Darfur

Yahouza S.MadobiJune 15, 2006

Babban alƙalin kotun ƙasa da ƙasa ta birnin Hage ya gabatar da rahoto a game da kissan kiyasun jama´a a yankin Darfur

https://p.dw.com/p/Btzi
Hoto: dpa

Shugaban kotun ƙasa da ƙasa ta Majalisar Ɗinkin Dunia mai kulla da lefikan yaƙi, ya gabatar da rahoto , gaban komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia.

Luis Moreno Ocampo, ya bayyana binciken da su ka gudanar a ƙasar Sudan a game da kashe -kashen jama´ar yankin Darfur.

Binciken da su ka gudanar ya bankado cewa kungioyin wanda suu ka kai hare ahren sun yi su da aniyar shafe yan kabilar Four,Massalit da Zaghawa.

Kuma ta sabawa dokokin yxancinrayuwar dan adama, ba tare da nuna wariyar ƙabila, da addini ko siyasa ba.

Shugaban wannan kotu, ya tabatar da cewa an shirya kissan kiyasu ga al´ummomin da ba su ji ba su gani ba, a yanki, kuma kotu zata ci gaba da bincike na zahiri, domin tantance masu leffi , ta kuma yanke masu hukunci da ya dace.

A ɗaya hannun rahoton na kotun Majalisar Ɗinkin Dunia, ya gano cewa, daga cikin mutane kimanin dubu ɗari 3, da su ka rasa rayuka, a yankin Darfur, da dama sun mutu sanadiyar yinwa da rashin kaukayan mahalli, bayan ƙona gidajen su, da dukiyoyin su.

Sannan, al ´ammuran fyaɗe sun zama ruwan dare a yankin.

A bayyanin da ya gabatar Luis Moreno Ocampo ya ce sun fuskanci matsaloli masu yawa wajen gudanar da binciken, wanda a halin yanzu, ya tsaya kawai a birnin Khartum.

A makon da ya gabata hukumar kare haƙƙoƙin jama´a, ta Human Rigts Watch, ta yi tsokaci, a game da tafiyar hawainiyar da kotun ƙasa da ƙasa ke yi, a kan shari´ar Darfur, sannan ta zargi hukumomin Khartum da girka, da girka wasu abu masu kama da kotuna, domin kulla da wannan shari´a.

Wannan kotuna, za su ƙara dagula al´ammur, domin a cikin ka´idojin kotun, Kasa da Kasa ta birnin Hage,ba ta da izinin gurfanar da wani mai leffi, muddun a ka riga a ka gurfanar da shi a ƙasar sa.

To amma babban alƙalin kotun Hage ya ce, har ya yanzu kotunan Sudan, sun gabatar da shari´a,ga mutane 13 kaɗai, daga wanda a ke tuhuma da kunna rikicin Darfur, kuma leffikan da a ka tuhume su da aikatawa,kwata- kwata, ba su shafi kissan kiyasu ba.

A game da haka, kotun ƙasa da ƙasa, na da damar gurfanar da su, a lokacin da ya dace.

A nasa ɓangare, wakilin Sudan, a Majalisar Dinkin Dunia, ya kare ƙasar sa, da cewar alƙalan cikin gida, na aiki tuƙuru, domin gano gaskiyar kasahe kashen Darfur.

Kuma tunni, har sun yanke hukuncin ɗaurin rai da rai, da ma na kissa, ga mutanen da a ka tabbatar da leffikan su.

Wasu daga membobin komitin sulhu sun bayyana gamsuwa da ayyukan kotun ƙasa da ƙasa, domin a tunanin su, idan kotun ta yi garajen gurfanar da hukumomin Sudan, da ta ke tuhuma da hannu a cikin al´ammarin, Khartum, ta sami hujjar ƙin amincewa, da karɓar tawagar dakarun shiga tsakani,ta Majalisar Ɗinkin Dunia, domin maye gurbin rundunar ƙungiyar Gamayya Afrika a Darfur.