1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

RAHOTON KUNGIYAR HADIN KAN TURAI GAME DA TURKIYYA

Yahaya AhmedNovember 6, 2003
https://p.dw.com/p/Bvnl

Kasar Turkiyya dai ta yi ta dokin jiran wannan rahoton, saboda mafi yawan al'umman kasar ne ke son su sani takamaimai, ko Hukumar Kungiyar Hadin Kan Turan na da niyyar karbar kasarsu cikin kungiyar ko kuma dai za ta ci gaba ne da yi mata saniyar ware. A jiya laraba ne aka gabatad da rahoton, wanda a bangare daya ya gamsad da wasu bangarori dake da jibinta da gwamnatin birnin Ankara.
Jami'an birnin Bbrussels dai sun nuna a cikin rahoton cewa, an sami gagarumin ci gaba a huskar siyasa a kasar ta Turkiyya, tun daga samun daman da `yan kasar suka yi na fadan albakacin bakinsu, ba tare da jin tsoron an dau wasu tsauraran matakai game da su ba, da samun damar yin zanga-zanga, da bai wa `yan tsiraru kamar Kurdawa `yancin bunkasa al'adunsu na gargajiya, da kuma ragen anngizon da sojin kasarr ke da shi kan zababbiyar gwamnatin dimukradiyya. Amma duk da wannan yabon daga birnin Brussels, Hukumar kungiyar Hadin Kan Turaita kuma bayyana inda har ila yau da a nata ganin Turkiyyan ba ta taka wata muhimmiyar rawar gani ba. Har ila yau dai, inji rahoton, Janar-Janar din rundunar sojin Turkiyan na ci gaba da yi wa harkokin siyasar kasar katsalandan. Bugu da kari kuma, al'umman Kurdawa na nan na ta jiran cika alkawarin da aka yi musu na samun damar watsa shirye-shiryensu a kann talabijan, da kuma yin amfani da harshensu a makarantu. Kawo yanzu kuma, ba a sami ci gaba wajen kawo karshen nuna wa fursunoni azaba a gidajen yari ba. Game da rahoton dai, ministan harkokin wajen Turkiyya Abdullah Gül, ya bayyana cewa, gwamnattinsa na bukatar karin lokaci don aiwatad da duk dokokin da majalisa ta zartar. A cikin watanni masu kuma, za a ga misali a zahiri, inji ministan.
Masu sukar lamiri dai na kyautata zaton cewa, a cikin `yan makwanni masu zuwa, Turkiyya za ta dau wasu matakai, ko da ma na nuna wa duniya wata alama ne, na cewar a shirye take ta shigad duk canje-canje da kasar ke bukata don ta sami karbuwa a cikin gamayyar Turai. Ana hasashen cewa, mahukuntan kasar za su sake bude makarantun kiristoci da da aka rurufe, da bude farkon tashar talabijin mai yada shirye-shiryensa cikin harshen kurdanci, da kuma sako wasu fursunonin da aka tsare su saboda dalilan siyasa. Duk wadannan dai matakai ne, da Turkiyyan ke sa ran cewa, idan ta dauke su, za su taimaka wajen yunkurin da take yi na samun karbuwa a cikin kungiyar Hadin Kan Turai,a shawarwarin da za a yi a shekra mai zuwa.
Har ila yau dai, babbar matsalar da Turkiyyan ba ta takalo ba tukuna, ita ce batun nan na tsibirin Cyprus. Ita dai Hukumar kungiyar Hadin Kan Turan, ta bayyana cewa, kasancewar tsibirin rabe a sassa biyu, da kuma mamayen da Turkiyya ke yi wa rabin tsibirin, matssaloli ne da za su iya gindaya wa ci gaban shawarwarin wani gagarumin shinge.
A Cyprus din dai, shugaban yankin da ke karkashin ikon Turkawan tsibirin, Rauf Denktash, ya sake nata daddagewarsa ga duk wani sabon yunkurin zartad da wasu kuduroi kuma kan tsibirin gaba daya. A nasa ganin, kasar Girka ce, ke dauke da alhakin ko menene ma zai wakana a tsibirin.
Babban kallubalen da mahukuntan birnin Ankara ke huskanta a halin yanzu, shi ne yadda za su shawo kan Denktash ya sassauta matsayinsa kan wannan batun.