1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton MƊD akan Cutar AIDS

November 24, 2009

Sama da mutane miliyan 33 ke ɗauke da ƙwayar HIV a duniya. Sai dai kuma duk da haka an samu koma-bayan yawan masu kamuwa da cutar yanzu haka

https://p.dw.com/p/KeRl
Allon nuna ƙyamar cutar Aids a birnin Washington na AmirkaHoto: DW

Hukumar lafiya ta duniya da kuma takwararta da ke yaƙi da Aids ko Sida sun wallafa wani rahoton haɗin guywa a yau ɗin nan kan halin da cutar ke cikki a doron ƙasa. Suka ce cutar ta Sida ta ja baya da kashi 17 daga cikin ɗari a duniya idan aka kwatanta da shekaru 8 da suka gabata.

A nahiyarmu ta Afirka ne dai a ka fi samun nasarar daƙile karsashin cutar ta aids ko sida a 'yan shekarun nan da suka gabata, domin kuwa an samu raguwar kashin 15 daga cikin 100 na adadin mutanen da suke harbuwa da ƙwayar cutar ta HIV a wannan shekarar da muke ciki. Hukumar yaƙi da cutar ta Aids ta nunar da cewa amfani da nau´o´in ƙwayoyin nan 3 da masu fama da cutar ke yi ne ya sa a ka daina fiskanatar yawan mace-macen masu ɗauke da ƙwayar cutar HIV ciki kuwa har da ƙananan yara. A daura da haka ma dai, rahoton ya ce ana fama da yaɗuwar cutar ta aids ko sida a ƙasashen gabacin Turai. Amma a duniya gaba ɗaya an samu raguwar yawan masu kamuwa da ƙwayar cutar ta HIV in ji Michel Sidibe, darektan ƙungiyar yaƙi da cutar Aids ta MƊD:

Straßenkinder Malawi AIDS Aufklärungsposter
Yaƙi da cutar Aids a MalawiHoto: DW

"An samu raguwar kashi 17% na sabbin kamuwa da ƙwayar cutar, hatta a Afirka ana samun kyakkyawan ci gaba. A shekara ta 2008 an samu raguwar yawan sabbin kamuwa da misalin mutum dubu 400 idan an kwatanta da bara waccan. Ana kuma saka kyakkyawan fata a binciken wata allurar riga kafi da ake yi. Gwaje-gwaje na farko da aka yi a Thailand na ba da ƙwarin guiwa, kamar yadda aka ji daga Shangai. To sai dai kuma har yau da sauran rina a kaba kafin a kai ga tudun na tsira."

AIDS vaccine Thailand
Nasarar gwajin maganin Aids a ThailandHoto: AP

'Yan luwaɗi da maɗigo, da kuma 'yan ci rani dake neman aiki a ƙasashen waje su ne ke sahun waɗanda suka fi fuskantar barazanar kamuwa da cutar in ji Bernhard Schwartländer daga ƙungiyar yaƙi da cutar Aids ta MƊD.

"A ƙasar China kaɗai akwai 'yan ci rani kimanin miliyan 120 zuwa miliyan 200 dake watangaririya a yankuna daban-daban na kasar kuma a sakamakon haka su kan yi shekaru da dama ba su sadu da iyalansu ba, kuma galibi jahilai ne ba su da ilimi. Akwai wuya a samu nasarar wayar da kan irin waɗannan mutane. Ɗaya matsalar game da China kuma ita ce kasancewar mutum ba ya da ikon neman magani sai a inda yake da rajista da mahukunta. A sakamakon haka 'yan ci ranin basu da ikon neman magani a yankunan da suke gudanar da ayyukansu in har sun kamu da ƙwayar cutar."

Ko da yake an samu ci gaba a matakan binciken maganin cutar ta Aids, amma akasarin masu ɗauke da ƙwayoyin cutar ba su da kafar cin amfanin lamarin in ji Peter Ghys shugaban sashen binciken cututtuka masu yaɗuwa na ƙungiyar yaƙi da cutar Aids ta MDD.

4.O-Ton Ghys

"A halin da ake ciki yanzu duka-duka yawan masu ikon neman magani tsakanin mutanen dake ɗauke da ƙwayar cutar a ƙasashe masu ƙaramin ƙarfi bai wuce kashi 42% ba. Hakan dai na ma'ana ne cewar sama da kashi 50% na masu cutar ba su da wata kafa ta neman magani."

Yankin Afirka da ke kudu da sahara na ci gaba da zama inda ƙwayar cutar ta sida ta fi yaɗuwa a duniya, domin kuwa kashi 72 daga cikin 100 na mutanen da ke fama da raɗaɗin cutar na da zama ne a wannan yanki. Sa´annan kuma kashi 72 daga cikin 100 na waɗanda suka rasa rayukan nasu duk 'yan asalin wannan yanki ne. Hasali ma dai, Swaziland da ke kudancin Afirka na ci gaba da zama ƙasar da ta fi kowace yawan masu fama da cutar domin kuwa kashi 24 daga cikin 100 na al´umarta ke fama da sida.

Mutane miliyon 60 ne alƙaluman hukumomin biyu suka nunar cewa sun harbu da ƙwayar cutar HIV a sassa daban daban na duniya a cikin shekaru 8 da suka gabata. Daga cikinsu kuwa miliyon 25 sun rasa rayukansu daga shekara ta 2001 zuwa yanzu.

Mawallafi: Muohamadou Auwal Balarabe

Edita: Ahmad Tijani Lawal