1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton MƊD akan Gudun Hijira

Tijani LawalOctober 6, 2009

Gudun hijira kan taimaka wajen kyautata makomar rayuwar da dama daga mutanen da lamarin ya shafa

https://p.dw.com/p/K04M
Shelkwatar Majalisar Ɗinkin Duniya a New YorkHoto: AP

Yawa-yawanci, mutane kan yi hijira ne domin kauce wa matsaloli na cikin gida kama daga yaƙe-yaƙe na basasa zuwa ga bala'i daga Indallahi ko taɓarɓarewar tattalin arziƙi, tattare da fatan kyautata makomar rayuwarsu a ƙetare. Tun kuwa abin da ya kama daga shekarar 1990 MƊD ke bin diddigin wannan ci gaba, inda a cikin rahotonta na bana ta mayar da hankali akan kawar da shinge ga masu neman yin ƙaura.

Ga mutane da dama a duniyar nan tamu hijira ta zama wata muhimmiyar kafa domin kyautata makomar rayuwarsu. Ta hanyar hijira su kan samu damar bunƙasa yawan kuɗaɗensu na shiga da kyautata kiwon lafiyarsu da nagartaccen ilimi ga 'ya'yansu. Massu hijirar sun haɗa da rukunonin mutane ne daban-daban kama daga manoma zuwa ga nes-nes da fursinonin siyasa da leburori da malaman kimiyya. Dukkan waɗannan rukunonin mutane suna daga cikin 'yan gudun hijira kusan miliyan dubu ɗaya, waɗanda ku dai sun tagayyara a ƙasashensu ko kuma suna kan hanyar ƙaura a ƙetare. Palavia Pansieri, mai haɗa kan ayyukan sa kai na MƊD tayi batu game da 'yan gudun hijira miliyan dubu ɗaya, waɗanda miliyan 740 daga cikinsu sun tagayyara ne a cikin gida.

"Duka-duka 'yan gudun hijira miliyan 214 ne ke neman mafaka a ƙetare. Akasarin 'yan gudun hijirar kan tsere ne zuwa ƙasashe maƙobta, zuwa ƙasashen da harshensu iri ɗaya ne kuma da ƙyar ake samun wani banbanci na addini ko al'adu tsakaninsu. Kuma daga cikin waɗannan 'yan gudun hijira miliyan 214, duka-duka kashi ɗaya bisa uku, wato miliyan 70 kan yi ƙaura daga wata ƙasa mai tasowa zuwa wata mai ci gaban masana'antu."

Rahoton na MƊD yayi bayani dalla-dalla a game da irin fa'idar da 'yan gudun hijirar kan samu. A binciken da aka gudanar an gano cewar 'yan gudun hijira daga ƙasashe matalauta kan samu kafar riɓanya yawan kuɗaɗensu na shiga har ninki 15 bayan sun hijira zuwa ƙetare. Kazalika yawan yaran da aka tura makaranta ya kan riɓanya sau biyu da kuma ƙayyade mace-macen yara har ninki 16. To sai dai kuma rahoton yayi tsokaci a game da kada a kuskura a mayar da hijirar ta maye gurbin taimakon raya ƙasashe masu tasowa. Flavia Pansieri ta ƙara da bayani tana mai cewar:

"'Yan gudun hijirar kan aika da wani ɓangaren na kuɗaɗen dake shiga hannunsu zuwa gida, waɗanda akan yi amfani da su wasu 'yan ƙananan harkoki na kasuwanci da kiwon lafiya da ba da ilimi ga yara da kyautata makomar jin daɗin rayuwar dangi. Wani abin lura a nan shi ne yawan abin da 'yan gudun hijirar ke aikawa gida ya ninka yawan taimakon raya ƙasa har sau biyu zuwa huɗu."

Ta la'akari da haka rahoton na MƊD ke yin kira da a sassauta manufofin karɓar 'yan gudun hijira. Rita Süssmuth, ƙwararriyar masaniya akan guje-gujen hijira kuma tsofuwar kakakin majalisar dokokin Jamus ta Bundestag tayi marhabin da rahoton na MƊD sannan ta ƙara da cewar:

"A halin da ake ciki yanzun babu wata ƙasa da zata iya warware matsalolinta ita kaɗai, walau matsalar 'yan gudun hijira ce ko ta kewayen ɗan-Adam da yunwa. Dukkanmu muna buƙatar juna."

Mawllafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita:Umaru Aliyu