1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton MDD akan kasashen Larabawa

April 7, 2005

A jiya laraba hukumar MDD akan manufofin raya kasa UNDP ta gabatar da rahotonta akan halin da ake ciki a siyasar kasashen Larabawa

https://p.dw.com/p/BvcW

A cikin rahoton nata hukumar MDD akan manufofin raya kasa ta kira kasashen Larabawa tamkar wani gungu na ‚yan kama-karya. Wannan rahoto mai taken "‘Yanci da kyakkyawan mulki a kasashen Larabawa, shi ne na uku da wata tawagar masana al’amuran zamantakewa na kasashen Larabawa ta gabatar. Kuma ko da yake shuagabannin kasashen dake mulkin kama karya su kan yi ko oho da ire-iren wadannan rahotanni, amma a bisa ga ra’ayin Nader Ferghani, shugaban tawagar ta hukumar MDD UNDP da ta gudanar da wannan bincike, wannan wata sabuwar manufa ce ta musamman, inda ya kara da cewar:

Tuni wasu kalmomin da aka yi amfani da su a wadannan rahotanni suka cikin jerin kalmomin da gwamnatocin kasashen Larabawa ke amfani da su a cikin jawabansu. Misali a kasar Masar gwamnati na amfani da taken rahoto na biyu da aka gabatar a can baya, wanda ke ma’anar ilimantar da jama’a a cikin jawabanta. Wani abin mamaki ma ita kanta gwamnatin sai da ta ba wa wani taron bitar manufofin garambawul ga manhajar ilimi a kasar taken "Akan hanyar yada ilimi tsakanin jama’a". Wato ke nan kwalliya ta mayar da kudi dangane da burin da ake neman cimmawa a rahoton na baya.

  • A cikin rahoton da aka gabatar a ranar larabar da ta wuce an tabo batun ci gaban da ake samu na canjin salon tunanin gwamnatocin kasashen Larabawa da kuma ba da la’akari da muhimmancin aiwatar da garambawul, musamman ma idan aka lura da zanga-zangar adawa da aka rika fuskanta a Lebanon da Masar ko zaben kananan hukumomi a Saudiyya da kuma shawarar baya-bayan nan da shugaba Hosni Mubarak ya bayar game da samun ‚yan takara barkatai da zasu tsaya zaben shugaban kasar Masar da za a gudanar nan gaba a wannan shekara. To sai dai kuma rahoton ya kara da bayanin cewar wannan ci gaba baya ma’anar cewar shugaba Bush na Amurka ya cimma biyan bukatarsa ta yada mulkin demokradiyya a Yankin Gabas ta Tsakiya, duk kuwa da cewar an samu wasu masana na kasashen Larabawa dake sukan lamirin mawallafan rahoto da ba wa Amurka goyan baya. Amma a hakika shi kansa rahoton yayi Allah Waddai da manufofin Amurka dangane da Yankin Gabas ta Tsakiya, kuma wannan shi ne ainifin dalilin da ya sanya Amurkan da wasu kasashe na Larabawa suka ki yarda da a gabatar da rahoton akan kari, suna masu neman ganin an yi karin bayani da cewar ra’ayin da aka bayar a rahoton dai ba ya dauke da tambarin MDD ko hukumarta akan manufofin raya kasa. Amma duk da haka rahoton tamkar gangami ne ga kasashen Larabawa domin hamzarta daukar kwararan matakai na garambawul tun kafin al’amura su kara rincabewa a kuma tsunduma cikin wani mawuyacin hali na kaka-nika-yi a shiyyar Gabas ta Tsakiya baki daya.