1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton Oxfam a game da cinakin Harssasai a dunia

June 15, 2006
https://p.dw.com/p/Butw

A ƙalla harssasai billiard 14, a ke ƙerawa ko wace shekara a dunia, wannan alƙalluma sun hito daga wani rahoto, da ƙungiyar Oxfam ta bayyana a sahiyar yau alhamis.

Wannan rahoto ya hito, a yayin da ya rage yan kwanaki ƙalilan, Majalisar Dinkin Dunia, ta yi zaman taro, a dangane da batun sapara makamai tsakanin ƙasa da ƙasa.

Oxfam ta zargi Majalisar a game da halin ko in kula, da ta ke nunawa, a game da wannan matsala, da ke umal mutuwar dubun dubunnan jama´a, a ko wace shekara.

Ƙungiyar ta ce, idan a ɗauki misalin ƙasar Irak, akwai bindigogi da harssassai, baje cikin kasuwa, da mutane ke saya da kuɗaɗen da, basu wuce dalla 2 da rabi ba.

Hakan na wakana, sanadiyar sakacin Majalisar Ɗinkin Dunia, wajen kula da shigi da ficin makamai da harssasai.

A cikin wannan rahoto, Oxfam ta ce, a ƙalla ƙasashe 76 na dunia, a halin yanzu, ke ƙera harssasai, wanda suka shahara wajen sayar da su, sun haɗa da China, Masar, Iran, Brasil, Roumania, Bulgaria da Israela.