1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton shekara na ƙungiyar kare haƙƙoƙin bani adama ta FIDH

March 21, 2006
https://p.dw.com/p/Bv4O

Hukumar kare haƙƙoƙin bani adama ta ƙasa da ƙasa, wato FIDH ko kuma IFHR, ta gabatar da rahoton ta, na shekara a a game da yadda membobin ƙungiyoyin fafatakar neman yancin jama´a ,su ka gudanar da ayyuka a shekara ta 2005.

Rahoto, ya ce, mutane 117 ne masu fafatakar kare haƙƙokin jama´a, a ka kashe har lahira ,a sassa daban daban na dunia a wannan shekara.

ƙasar Colombia, ta fi ƙaurin suna, ta wannan fanni, inda yan kishin haƙin bani adama 47 su ka rasa rayuka.

Shugaban hukumar Sidiki Kaba ,ya nuna mattukar damuwa a game da hauhawan barazanar kissa ga membobin su

Wannan rahoto, ya bi diddiƙi, ƙasa da ƙasa, inda ya jera kasashe kamar su Iran, China, Sudan, Tunisia, da dai sauran su, a sahun ƙasashe, inda yan kadin, kare haƙokin jama´a ke fuskantar azaba, da yawan barazanar kissa.