1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton Shekara Na Cibiyar IISS

October 20, 2004

A jiya talata ne cibiyar nazarin manufofin tsaro ta kasa da kasa dake birnin London ta gabatar da rahotonta dangane da shekara ta 2004 da shekara ta 2005

https://p.dw.com/p/BvfQ

A cikin rahoton nata dangane da shekara ta 2004 da ta 2005, cibiyar nazarin manufofin tsaro ta kasa-da-kasa IISS dake birnin London ta ce rikicin kasar Iraki da ya ki ci ya ki cinyewa ya kara tsaurara matakan ta’addanci akan kasashen yammaci. Bisa ga dukkan alamu kutsen da aka yi wa kasar ta Iraki ya taimaka wa kungiyar Al’Ka’ida da sauran kungiyoyi masu tsananin kishin addini wajen samun karin magoya baya a matakansu na jihadi.John Shipmann, darektan cibiyar ya ce ko da yake a halin da ake ciki yanzu shuagabannin Al’Ka’ida guda biyu Osama bin Laden da Ayman Azzawahiri ba su da alaka kai tsaye da magoya bayansu, amma kungiyar tana nan daran dakau tana kuma da ikon gudanar da ayyukanta. Cibiyar ta IISS ta kara da bayanin cewar har yau kasar Iraki na fama da mummunan gibi na tsaro, lamarin dake ba wa kungiyoyi masu tsananin kishin addini wata dama ta yakar gwamnatin da a ganinsu haramtacciya ce ta jeki-na-yi-ki. Akwai bukatar daukar wasu matakai guda uku domin sake dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan kasa. John Shipman ya kara da cewar:

Da farko dai abu mafi muhimmanci shi ne dora alhakin maido da doka da odar a hannun su kansu jami'an tsaron kasar Iraki. Sannan na biyu a sakarwa da gwamnati cikakkiyar dama ta gudanarwa a cikin gaggawa. Sannan na uku wajibi ne a shigar da ‚yan tsagerar kasar ta Iraki a dukkan shawarwarin da ake gudanarwa ta yadda zasu kai ganon cewar bin manufofi na siyasa shi ne a’ala akan matakan ta da zaune tsaye.

A dai halin da ake ciki yanzu kasar Koriya ta Arewa, wata barazana ce ta musamman ga makomar zaman lafiyar duniya. Bisa ga dukkan alamu kasar na da isasshen ma’adanin Plutonium, wanda zai ba ta kafar sarrafa karin makamai na kare-dangi. Dukkan shawarwarin da aka gudanar tare da tsoma bakin kasar China basu samar da kusantar juna ba, ballantana a kai ga wata yarjejeniyar kakkabe kasar Koriya ta Arewar daga muggan makamai na kare dangi.

Daya maganar da rahoton cibiyar ta nazarin manufofin tsaro ta kasa da kasa dake birnin London ya kunsa kuma shi ne yawan kudaden da kasashe ke kashewa akan matakan tsaron kansu. A wannan bangaren an samu karuwar kashi 15% a tsakanin shekara ta 2002 da shekara ta 2003. Amurka ce ke da rabon kashi biyu bisa uku na wannan adadi, a yayinda kasashen Turai suka samu dan koma baya, in banda Birtaniya. A lokacin da yake bayani Alex Nicoll, mataimakin darektan cibiyar cewa yayi:

Ga alamu dai ita Amurka ta dukufa ne wajen karfafa matsayinta na soja a matsayin wata babbar daula ta duniya. Amma fa hakan ba ya nufin cewar kasar na da ikon daukar wani nagartaccen mataki mai ma’ana bisa manufa. Su kuwa kasashen Turai sun fi sha’awar hanyoyi na lumana. A saboda haka suka fara karkata wajen kirkiro ruduna ta musamman a maimakon sabunta fasahar makamansu.