1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton Shekara Na Hukumar Raya Kasa Ta MDD

July 15, 2004

Tun abin da ya kama daga shekarar 1990 Hukumar Raya Kasa Ta MDD ke gabatar da rahotanninta na shekara dangane da irin ci gaban da ake samu a fannoni dabam-dabam na rayuwar dan-Adam a duk fadin duniya

https://p.dw.com/p/Bvi7

A cikin rahotonta na bana hukumar raya kasa ta MDD ta mayar da hankalinta ne akan dangantakar al’adu a sassa dabam-dabam na duniyar. Bisa ga ra’ayin hukumar kyautata dangantakar al’adu domin zama wani bangare na manufofin kare hakkin dan-Adam shi ne zai taimaka wajen kyautata cude-ni-in-cude-ka tsakanin jinsunan mutane da kabilu masu banbancin al’adu a wannan karni na 21 da muke ciki yanzun, musamman ta la’akari da gaskiyar cewar kimanin kashi biyu bisa uku na illahirin kasashen dake doron duniyar nan tamu suna kunshe da kashi 10% na tsirarun kabilu tsakanin al’umarsu. Hukumar ta ce wajibi ne dukkan kasashen su gabatar da nagartattun matakai domin yaki da kabilanci ko wata manufa ta wariya sakamakon banbance-banbancen al'du da addini ko yare. Wakiliyar Jamus a hukumar ta MDD Gabriele Köhler ta ce a ganinta ‚yancin gudanar da al’adu na fuskantar barazana a kasashe da dama dake tasowa, musamman ma a bangaren yare da addini. Babban misali, kamar yadda yake kunshe a cikin rahoton, shi ne a kasar Thailand akwai wasu kabilun, mazauna yankunan tsaunukan kasar, wadanda ba su da hakkin kada kuri’a a zabubbukan wannan kasa saboda kasancewar suna amfani ne da wasu harsuna dabam. Akwai kasashe da dama dake fama da irin wannan matsala, abin da ya hada har da kasashe da dama dake da ci gaban masana’antu. Ita ma ministar taimakon raya kasashe masu tasowa Heidemarie-Wieczorek-Zeul tana tattare da ra’ayin cewar kyautata makomar rayuwar jama’a shi ne kawai zai kara ba su cikakken ‚yancin tofa albarkacin bakinsu da kuma shiga ana damawa da su a muhimman manufofin raya kasa. To sai dai kuma ta kara da cewar bai kamata a yi amfani da ‚yancin al’adu ko na addini domin zama wata kafa ta danne hakkin mata ba. Wajibi ne manufar girmama hakkin dan-Adam ta zama ginshikin duk wata alakar da zata samu tsakanin mutane a wawware.Wannan maganar ita ce ta fi ci wa wakiliyar Jamus a hukumar ta MDD tuwo a kwarya, inda a ganinta akwai masu fakewa da guzuma domin su harbi karsana, inda suke batu a game da al’adunsu na gargajiya ko batutuwa na addini domin tauye wa mata hakkinsu. Rahoton hukumar ta MDD ya ba da shawarwari da dama a game da nagartattun matakan da za a iya dauka domin kyautata cude-ni-in-cude-ka tsakanin kabilu domin zama kasa daya al’uma daya, misali a nan Jamus ana iya ba wa baki damar shiga zabubbuka na kananan hukumomi da damar rike takardun fasfo na kasashe biyu. Kasashe da dama, kamar yadda Gabriele Köhler ta nunar ba zasu ji dadin wannan rahoto ba, amma ainifin makasudin gabatar da shi shi ne domin dasa harsashin mahawara da ba wa ayyukan hukumar wani tsayayyen fasali a alakarta da gwamnatoci da kuma kungiyoyi masu zaman kansu a kasashen da lamarin ya shafa.