1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton shekara na kungiyar taimakon abinci ta Jamus

June 29, 2005

Kungiyar taimakon abinci ta Jamus Brot für die Welt ta samu gudummawar kudi na Euro miliyan 54 domin tafiyar da ayyukanta a shekarar da ta wuce

https://p.dw.com/p/Bvb1

A lokacin da take gabatar da rahoton na shekara, darektar kungiyar taimakon ta mujami’ar Evangelikan Cornelia Füllkrug-Weitzel ta ce babbar manufar da kungiyar ta Brot für die Welt ta sa gaba shi ne yaki da matsalar talauci, ganin yadda ake fama da tafiyar hawainiya a game da burin da MDD ta sa gaba dangane da karni na 21 da muke ciki yanzun. An samu karuwar yawan matalauta ‘yan rabbana ka wadata mu a kasashe da dama na Afurka dake kudu da hamadar sahara. Daya daga cikin dalilan wannan mummunan ci gaba shi ne mayar da hankali kacokam da aka yi wajen zuba kudaden jari a wuraren da ake kyautata zaton samun kazamar riba, a maimakon zuba kudaden a yankunan da ake fama da talauci, bisa manufar sassauta radadinsa ga talakawa. Kungiyar ta Brot für die Welt, wacce ta dogara kacokam akan kudaden gudummawar taimako daga jama’a ta fi ba da la’akari ne ga matakin taimakon kai da kai. A misalin shekaru biyu da suka wuce kungiyar ta gabatar da matakin bin diddigin musabbabin yunwa daga tushensa domin ta tantance matakan da suka fi dacewa wajen magance wannan matsala. Sakamakon binciken, kamar yadda aka ji daga bakin Cornelia Füllkrug-Weitzel, ya bayyanar a fili cewar masu fama da matsalar sun hada har da matasa masu jini a jika, wadanda galibi suke zaman kashe wando da ‘yan gudun hijira da marayun da suka yi asarar iyayensu sakamakon cutar Aids. A saboda haka a ganinta ya zama wajibi a tinkari matsalar daga tushenta. Kungiyar Brot für die Welt na tattare da ra’ayin cewar babu wani banbanci tsakanin taimakon jinkai da taimakon raya kasa. Wajibi ne dukkan matakan guda biyu su tafi kafada-da-kafada da juna. A sakamakon haka kungiyar ta koma karkashin tutar gamayyar taimakon mutane dake cikin mawuyacin hali, wacce ke bakin kokarinta wajen fahimtar da mutane muhimmancin hada kan manufofin na taimakon jinkai da taimakon raya kasa. Kungiyar dake karkashin inuwar mujami’ar Evanjelikan tana hadin kai da ainifin mutanen da lamarin ya shafa wajen binciko bakin zaren warware matsalolinsu na rayuwa. Bisa ga ra’ayin darektar kungiyar cutar Aids mai karya garkuwar jikin dan-Adam na daya daga cikin ummal’aba’isin yaduwar matsalar yunwa a yankunan karkara na kasashen Afurka, inda mutane suka dogara kacokam akan ayyukan noma. Gaba daya dai kamar yadda Cornelia Füllkrug-Weitzel ta nunar, muhimmin abin dake akwai shi ne a ba da la’akari sosai da sosai wajen yakar matsalar talauci a matakan taimakon raya kasashe masu tasowa. Akwai masu ikirarin cewar zuba kudaden jari shi ne kawai zai taimaka a shawo kan wannan matsala. Amma fa wani abin lura shi ne irin wannan mataki kan kai ga rushe gidajen mutane a yankunan da galibi mazauna cikinsu ‘yan rabbana ka wadata mu ne, wadanda bayan an fatattakesu daga wadannan yankuna zasu samu kansu cikin mawuyacin halin da ya zarce wanda suka kasance a ciki, kamar yadda ya faru a Mumbai ta kasar Indiya. Wannan ba mataki ne na yaki da talauci ba, mataki ne na yaki da matalauta.