1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton shekara na kungiyoyin Red Cross da Red Cresent akan balaoi a duniya

Hauwa Abubakar AjejeOctober 5, 2005
https://p.dw.com/p/BvZA
Hoto: AP

Rahoton na hadin gwiwa yace rashin hanyoyin yiwa jamaa gargadi ya sanya dubban mutane suka rasa rayukansu cikin annoba da tazo daga idallahi,musamman a lokacin ambaliyar ruwa ta tsunami a bara sai kuma balaoin mahaukaciyar ruwa da ambaliyar ruwa da ta haddasa.

Shugabar gudanarwar kungiyar agaji ta Red Cross Susan Johnson a lokacinda take kaddamar da rahoton tace hanyoyin yada labarai da yiwa jamaa gargadi suna da muhimmanci domin kuwa zasu ceci rayukan jamaa da dama.

Rahoton wanda ya shafi fari,karanciin abinci,girgizar kasa,ambaliyar ruwa da sauran balaoi,yace a 2004 mutane 250,0000 suka rasa rayukansu,cikin balai iri dabam dabam har guda 719.

Yawan wadannan mutane ya dara yawan mutane dake rasa rayukansu 67,000 a kowace shekara tun daga 1994-2003 musamman sakamakon tsunami wanda yayi sanadiyar mutane 225,000.

Akalla mutane miliyan 146 wadanan balaoi suka shafa,miliyan 110 sakamakon ambaliyar ruwa a kasashen Bangladesh,India da Sin.

Dukiyoyi da suka salwanta an kiyasta kudinsu ya kai tsakanin dala biliyan 100 zuwa 145.

Editan rahoton Jonathan Walter,yace samun hanyoyin sadarwa da yada labarai na zamani suna da muhimmanci,tunda acewarsa wani dan kasar India dake da zama a kasar Singapore ya sanarda iyayensa tahowar tsunami saboda rahotanni da yake samu daga kafofin yada labarai wanda hakan ya ceci rayukan akalla mutabe 3,600 da suka yankin da iyayen nasa suke.

Kodayake masana kimiya na India sun hango tahowar tsunami amma basu da naurorin zamani da zasi iya sanarda miloyoyin mutane dake kusa da tekun India.

Rahoton ya tabo batun mahaukatan guguwa na Charley,Frances,Ivan da Jeanne wadanda suka ratsa yankunan Karibiyan.

A lardin Dominica,mahaukaciyar guguwar Jeanne ta kasha mutane 4,amma an kwashe jamaa da dama daga yankunan,saboda wani shirin yada labarai day a taimakawa yawancisu.

Kodayake a kasar Haiti makwabciya saboda rashin hanyoyin sadarwa mutane 2000 sun halaka a wancan lokaci.

A kasar Jamaica kuma wadda ta gudanar da taron wayar da kan jamaa akan mahaukaciyar guguwa,wata guda kafin guguwar Ivan,maaikatan agaji na Red Cross sun taimaka kwashe mutane daga kan hanyar guguwar,inda anan mutane 17 suka rasa rayukansu.

Wadansu maaikatan agajin kuma suna taimakawa ne wajen kwantar da hankalin mutane da suke cikin tsoro da zulumi bayan abkuwar wadannan balaoi.

Inda a kasar Sri lanka maaikatan agajin sun taimaka wajen wayar da kan jamaa bayan abkuwar vtsunami inda da yawa daga cikin jamaar yankin suke ganin cewa ambaliyar,ta nuna hushin Allah ne bisa wasu laifuka da suka aikata.

Rahoton yace shirye shirye na wayar da kan jamaa zasu taimaka wajen yakar camfe da ake danganta su da irin wadannan balaoi.

Rahoton race ya kamata kuma a rika sanya jamaa na yankunan da abin ya shafa cikin shirye shiryen agaji,inda ya yi misali da kuskure da akayi wajen aiyukan rabar da kayayiyakin agaji a lokacin tsunami.

Rahoton yaci gaba da cewa dole ne cibiyoyin agaji su inganta hanyoyinsu na yada labarai da wayar da kan jamaa tare da inganta hadin kai tsakaninsu da alummomin da balai ya shafa.