1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton shekara na UNDP

November 9, 2006
https://p.dw.com/p/Bucj

Hukumar Majalisar Dinkin Dunia mai kulla da ci gaban ƙasashe, ta bayyana rahoton na shekara, a game da alamomin rayuwar al´umomin dunia.

Kamar yadda ta saba ako wace shekara, hukumar UNDP, ta bi ƙasashe daban-daban na dunia, domin gudanar da bincike, a kan yadda al´ummomin ke gudanar da rayuwa.

Binciken ya jiɓanci al´ammuran karatu, kiwon lahia, daɗewa a dunia,da dai sauran abubuwan more rayuwa.

Daga sahun ƙasashe 177 da UNDP Nowe ke kan gaba wajen kauttata rayuwar jama´a.

Daga ita sai,bi da bi sai ƙasashen Island, Australia, Irland da Sweden.

Kasar Amurika ke riƙe da matsayi na 8 .

Kamar ko wace shekara, a bana ma, rahoton UNDP ya nunar da cewa, al´ummomin ƙasashen Afrika, na fama cikin uƙubar rayuwa.

Daga jerin ƙasashen 177 Jamhuriya Niger ke sahun ƙarshe, sai kuma Saleo, Mali, Burkina Faso, da Guine Bissao, wanda su ka ɗan tsere mata.