1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton UNCTAD a game da nahiyar Afrika

Yahouza Sadissou MadobiSeptember 22, 2006

Hukumar cinaki da rayuwar ƙasashe ta bayana rahoton shekara , a game da nahiyar Afrika

https://p.dw.com/p/Bty3

Hukumar Majalisar Ɗinkin Dunia mai kulla da harakokin kasuwanci, da rayuwar ƙasashe, wato UNCTAD, ta bayyana rahoton ta, na shekara a game da yanayin ci gaban ƙasashen Afrika.

Hukumar UNCTAD ko kuma CNUCED, na da cibiyar ta, a birnin Geneva na ƙasar Suizland, kuma ta na ɗaya, daga cikin hukumomin kulla da tattalin arziki, a Majalisar Dinkin Dunia.

Ranar jiya ne wannan hukuma ta bayyana rahoto ,wanda ya ƙunshi ci gaba, ko akasin haka, da Afrika ta samu ta fannin tattalin arzikin a shekara ta 2005.

A taron manema labarai da ya kira domin bayana wannan sakamako, wakilin mussamnan na UNCTAD mai kulla da nahiyar Afrika, Kamran Kousari ya ce daga samun yancin kan mafi yawan ƙasashen Afrika a shekara ta 1960, zuwa yanzu, sun samu kuɗaɗen taimako daga ƙetare, wanda yawan su ya kai kussan dalla milion dubu ɗari 6.

To saidai duk da wannan magudan Kudi har yanzu Afrika ta kasa cirawa, kamar sauran ƙashen dunia domin ingata rayuwar al´ummomin ta.

A ta bakin Kamran Koussari, hakan ya biyo bayan harakokin siyasa tsagwaro, da ke tattare da agajin da ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki, ke ba Afrika, da kuma matakin bani gishiri in baka manda.

Mafi yawan ƙasashen na bin sa ransu ,wajen bada taimakon ko da bai dace ba da buƙatocin al´ummomin Afrika.

Jami´in ya bada misalin ƙasar Tanzania, wadda a halin yanzu, ke matsayin yar lellen ƙasashen masu hannu da shuni.

Tanzania, ta ƙunshi ƙungiyoyin bada agaji na ƙasa da ƙasa,fiye da 250, da su ke kishin junan su, tare da gita sharuɗa ga hukumomin ƙasar, kamar yaƙi da cin hanci da rashawa, yaƙi da talauci da kuma cuttutukan ƙajamau , massara cizon sabro da dai sauran su.

Duk da yawan wannan kafofi bada taimako, har yanzu Tanzania na matsayin ta ,na ƙasa mai fama da talauci.

Ya ce a lokacin yaƙin cecar baka, ƙasashen yammacin dunia sun yi anfani matuka gayya, da siyasa kamin su kai tallafi zuwa wata ƙasar Afrika.

A halin yanzu da yaƙin cacar baka ya kau,sun kuma sa yaƙi da ta´danci a gaba.

A game da haka, ƙasar da ta fi bada haɗin kai wajen wannan yaƙi, ta fi cin gajiyar taimako.

Idan aka duba zuzunrutun kuɗaɗen da Amurika ke kashewa a Afghanistan, Pakistan, Iraki da Turquia,lalle kai ka kace abin akwai lauje cikin naɗi inji Kamran Kousari.

Lokaci yayi, a daidaita sahun tallafin da Afrika ke samu, ta yadda zai anfanin jama´ar da a keyi don su.

Hukumar UNCTAD ta bada shawara tattara dukan taimakon a wata gidauniya ta musamman, bisa kullar MDD.

Sannan Majalisar ta girka komitin ƙurraru, wanda zai bi diddiƙin matsalolin ko wace ƙasa ta Afrika, domin ya raba taimakon daidai ruwa daidai tsaki.