1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton Unicef a game da mutuwar ƙananan yara a dunia

September 13, 2007
https://p.dw.com/p/BuBY

Hukumar Majalisar Ɗinkin Dunia mai kulla da ƙananan yara, wato Unicef, ta bayyana rahoto a game da halin da yaran ke cikin dunia.

Wannan rahoto ya nunar da cewa, an samu ci gaba mai inganci, ta fannin rage yawan mace-macen ƙanana yara.

Yawan yaran da su ka mutu a sanadiyar cuwarawarta daban-daban a shekara da ta gabata, shine mafi ƙaranci tun shekarau 17 da su ka wuce.

Saidai wannan cigaba ya banbata, daga wannnan ƙasa zuwa wacen, sannan daga wannan nahia zuwa wacen.

A cewar hukumar Unicef, an cimma wannan kyaukyawan sakamako, a dalili da matakan da a ka ɗauka na waye kan jama´a, a game da mahimancin shayar da jarirai nono iyayen su, da kuma allurai riga kafi na cututukan gynda, da anfani ga gidajen sabro.

Rahoton ya yabawa wasu ƙasashen nahiyar Afrika, a game da nasara da su ka samu ta wannan fannin. Wannan ƙasashe sun haɗa da Malawi, Ethiopia, Jamhuriya Niger, Namibia da Tanzania.