1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton unodc game da laifuffuka a nahiyar Africa

ibrahim saniMay 18, 2005

Matsaloli da suka dabaibaye da yawa daga cikin kasashen Africa

https://p.dw.com/p/Bvbv
Hoto: AP

Rahoton wanda darekta mai cikakken iko dake lura da wannan hukuma,wato Antonio Maria ya kaddamar a Abujan Nigeria ya tabo abubuwa da daman gaske dake ciwa kasashen nahiyar ta Africa tuwo a kwarya.

Da farko dai rahoton yace a tsawon shekaru goma da suka gabata nahiyar Africa tafi kowace nahiya a duniya fuskantar rikice rikice da suka danganci yake yaken basasa da makaman tansu.

Bugu da kari rahoton yaci gaba da cewa ba a da bayan haka akwai kuma rashin kyakkyawan tsaro dake addabar da yawa daga cikin kasashen sakamakon miyagun aiyuka daga wasu batagari a wasu kasashe na African.

Har ila yau rahoton ya kuma danganta rashin ci gaban da kasashe masu tasowa basa samu yadda ya kamata da matsaloli da suka hada da rashin daidaito na yadda wasu kasashe ke kashe kudaden shigar su a hanyoyin wadata yan kasa da abubuwan more rayuwa.

Bugu da kari rahoton wanda shine irin sa n a farko game da nashiyar ta Africa ya kuma yi tsokaci game da yadda rashin kyakkyawan tsaro da rashin doka da oda ke hana yan kasuwar kasashen ketare sa hannun jarin su a cikin kamfaninnika da kuma masana,antu a nahiyar.

Kai bama yan kasuwa daga kasashen waje bama da yawa daga cikin yan kasar a cewar rahoton sun fi son saka hannun jarin su a wasu kasashe dake wajen Nahiyar domin a ganin su hankalin su yafi kwanciya a maimakon saka hannun jarin a kasashen su.

Wan nan matsala a cewar Rahoton ta taimaka wajen saka tattalin arzikin wasu kasashe da dama na nahiyar a cikin halin kaka ni kayi,wanda hakan ya kara haifar da rashin aikin yi gada yawa dagac cikin miliyoyin matasa a nahiyar.

A waje daya kuma bankin duniya ya tabbatar da cewa batun cin hanci da rashawa da a yanzu ya kusan zamowa ruwan dare a kusan da yawa daga cikin kasashen nahiyar ya taimaka kwarai matuka wajen kara jefa kasashen a cikin halin la,ula ha ula,i na rashin sanin inda aka dosa game da ci gaba mai ma,ana.

Haka shima asusun dake tallafawa kana nan yara na mdd wato Unicef a turance yace kashi 89 daga cikin dari na kasashen Africa a yanzu haka na fama da matsalar safarar bil adama,ko dai izuwa kasashen ketare ko kuma a matsayin zangon da ake tara su kafin wucewa dasu izuwa inda za a kaisu.

Duk da wadan nan tarun matsalolin rahoton a karshe yace akwai alamun cewa a yanzu haka wasu daga cikin kasashen na Africa sun fara tunkarar wadan nan manya manyan kalubalen dake gaban su.

Wadan nan matakai kuwa a cewar rahoton akwai daukar matakan bunkasa tattalin arziki da inganta mulkin dimokradiyya da kuma daukar matakan yaki da aiyukan cin hanci da kuma rashawa kana a hannu daya da batun tabbatar da doka da kuma oda.

A daya hannun kuma rahoton ya yabawa gwamnatin Nigeria karkashin shugaba Olesegun Obasanjo game da kokarin da take wajen daukar matakan yaki da aiyukan cin hanci da kuma rashawa.

Ita kanta kungiyyar hadin kann nahiyar Africa wato Au da kuma wasu kungiyoyi masu zaman kansu a wasu kasashe a nahiyar sun samu irin wan nan yabo game da irin kokarin da suke wajen ganin an samu kyakkyawan tsaro don samun kwanciyar zaman lafiya a nahiyar baki daya.