1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton Worldwatch na shekara

April 27, 2005

A yau aka gabatar da rahoton shekara na cibiyar Worldwatch ta kasar Amurka akan kewayen dan-Adam da al'amuran tsaro a duniya

https://p.dw.com/p/BvcG
Joschka Fischer
Joschka FischerHoto: AP

A lokacin da yake jawabi dangane da bikin gabatar da rahoton na cibiyar Worldwatch da aka fassara zuwa harshen Jamusanci a fadar mulki ta Berlin, ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer ya ce wannan take da aka ba wa rahoton ya dace matuka ainun, saboda maganar tsaro ita ce ta dabaibaye yanayin siyasar duniya yanzu haka. Maganar tsaron, a hakika, ba kawai ta shafi manufofi ne na soja ba, kazalika ta hada da kare makomar kewayen dan-adam da girmama hakkinsa da kuma mulki na demokradiyya. Bisa ga ra’ayin Fischer wannan rahoton ka iya zama wata madogara a game da irin ci gaban da za a samu a fannin tsaro da zaman lafiya da kwanciyar hankalin duniya baki daya a cikin karnin nan na 21. Duk da ci gaban da nahiyar Turai take samu a kokarinta na hadin kann kasashenta, amma ba zata yiwu ta kebe kanta waje daya tana mai zura ido akan sauran kasashen dake makobtaka da ita suna masu fama da tashe-tashen hankula na siyasa da kabilanci da kuma koma bayan tattalin arziki ba. Wajibi ne kwanciyar hankalin da wadatar duk su yadu su hada da sauran kasashen dake gabar tekun baharrum. Duk wani mataki da nahiyar Turai zata dauka domin shingence iyakokinta ba zai tsinana kome ba, sai dai fa ta nemi hadin kai tare da kyautata ma’amallarta da kasashen yankin tekun baharrum. Ministan harkokin wajen na Jamus sai ya ci gaba da cewar:

Ba kawai a saboda dalilai na tarihi ba, muddin muna fatan tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a nahiyar Turai, to kuwa wajibi ne mu kara karfafa hadin kai da kuma kawo sauyi ga dangantakar kasa da kasa. Kazalika wajibi ne mu kara karfafa matsayin kafofi na kasa da kasa, kamar dai MDD a maimakon dogara kacokam akan wata babbar daula ta duniya.

A daya bangaren shugaban cibiyar ta Worldwatch Chris Flavin ya bayyanar a fili dangantakar dake akwai tsakanin matsalolin tattalin arzikin da ake fama dasu a sassa daban-daban na duniya yanzu haka da kuma matsalolin tsaro. Sai ya ci gaba da cewar:

An kiyasce cewar matasa masu jini a jika kimanin miliyan 200 ne ke zaman kashe wando a sassan duniya daban-daban. Sannan a daya bangaren kuma kasashen Asiya da na Latin-Amurka na fama da koma bayan haifuwa, a yayinda ake ci gaba da fama da bunkasar Jama’a a kasashen Afurka dake kudu da hamadar Sahara da kasashen Yankin Gabas ta Tsakiya da kuma na kudancin Asiya. A wadannan kasashe an fi fama da matsalolin guje-gujen hijira da zazzafan ra’ayin addini da barazanar ta’addanci.