1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rakuman daji sun fara bacewa a Nijar

September 28, 2016

Hukumomin Nijar sun dauki matakan kare ragowar rakuman dajin da suka rage a kasar sakamakon barazanar canjin yanayi da saran daji da al'ummar yankin Koure ke yi wanda ya kai ga takaita filayen kiwon namun dajin.

https://p.dw.com/p/2Qgqz
Niger Giraffen aus dem Kouré Giraffe Reserve
Hoto: Getty Images/AFP/B. Hama

 

Garin Koure dake kusa da Niamey na daya daga cikin kananan hukumomi hudu da Allah ya albarkanta da yanayi da rakuman daji ke bukata.Dama rakumman dajin da suka rage a yammacin Afirka na fuskantar barazanar bacewa. Dabbobin da kansu ne ke kokarin yi wa kansu abincin rana duk da tsallara zafin rana,

Ko wani daya na iya kai tsawon mita biyar da nauyin ton daya da kilogram 800,  kana ko kowani rakumin daji kan iya cin ciyawa danye ko furen ganyen itatuwa mai laushi akalla kilo talatin a tsawon kowane yini. Malam Sama'ila Arzika wanda shi ne jami'in da ke kula da rakuman dajin a garin Koure ya ce sun " kasance cikin yanayi mai kyau, babu tashin hankali, babu barazanar namun daji irin zaki da kura da ke neman cinyesu." 

Rakuman dawa na fama da matsaloli a Nijar 

Niger Giraffen aus dem Kouré Giraffe Reserve
Rakuman daji na samun abinci sosai a garin KoureHoto: picture-alliance/robertharding/Godong

Binciken da akayi a shekarun 2014 zuwa 2015 ya tabbatar da cewar akwai akalla rakumman daji sama da 500 dake rayuwa a wannan yankin na Jamhuriyar Nijar. Sai dai rakuman na fama da matsalar gurbatar yanayi duba da karin filin noma da saran itace da al'ummar yankin ke yi. Hakan ya takaitar da wurin kiyonsu daga Eka dubu 126 a shekarun 1996 i zuwa ga Eka dubu 86.

Duk da wadannan matsalolin dai  jama'a na zagaye da inda rakumman ke kiwo da sunan bude ido. Malam Siddo adamu wani dan kauyen ne na Koure da ya shafe sama da shekaru 26 ya na rayuwa da rakumman dajin, ya ce " A garin namu an yi abubuwa da yawa don an gina mana makarantu, ana kawo muna magungunna da sauran taimako da muke samu albarkacin rakumman dajin na. "

Gwamnatin Nijar na iyakacin kokarinta don kare sauran dabbobin dake da matukar tasiri ga afrika da kuma suka kasance irinsu mafi shauki da ban sha'awa fiye da na gabashin Afrika duba da irin fatar su da tarbiyarsu.