1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rana ta biyu a taron kolin kungiyar NATO a birnin Riga

November 29, 2006
https://p.dw.com/p/BuZn
Shugabannin kasashen kungiyar tsaro ta NATO sun fara taron kolinsu a Riga babban birnin kasar Latvia. Batutuwan da suka fi daukar hankali a taron na bana sun hada da halin da ake ciki a Afghanistan da kuma Iraqi. A jawabin bude taron sakatare janar na kungiyar ta NATO Jaap de Hoop Scheffer yayi kira ga kungiyar da ta kara yawan dakarunta musamman a kudancin Afghanistan. Kawo yanzu dakarun Birtaniya da na Kanada da kuma na NL ke fafatawa da mayakan Taliban a wannan yanki yayin da sojojin Jamus kuma ke kula da arewacin kasar, inda ake da kwanciyar hankali. Mista Scheffer ya ce ana bukatar karin sojoji dubu 2 da 500 don tinkarar rikicin da ke kara yin muni. Shi ma shugaban Amirka GWB ya yi suka ne ga kasashen dake dari-dari wajen tura dakarun su zuwa yankunan da ake fama da rikicin. Ita kuwa SGJ Angela Merkel ta ce ko da yake dakarun Jamus ka iya taimakawa a kudancin Afghanistan din amma ba wani dalili na kara yawan dakaru a yankin.