1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

RANA TA BIYU A ZAUREN MAJALISAR DUNKIN DUNIYA.

September 22, 2004

Batun Daftarin samar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya,ya sake samun waiwaye a taron koli na shekara shekara a zauren MDD.

https://p.dw.com/p/BvgG
Babban magatakardan Majalisar Dunkin Duniya Kofi Annan.
Babban magatakardan Majalisar Dunkin Duniya Kofi Annan.Hoto: AP

Acigaba da taron koli na MDD dake gudana a birnin New York din kasar Amurka,masu daukan nauyin daftarin nan na samarda zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya,zasu gana,domin nazari kann hanyoyi dazaa bi na kawo karshen rikicin Izraela da Palasdinu.

Majalisar dunkin duniya,da Amurka da kungiyar gammayyar turai da Rasha ,zasu gana ne ayau ,a gefen babban taron shekara shekaran,dangane da shakku da ake yanzu dangane da yiwuwan warware rikicin na gabas ta tsakiya dayaki ci yaki cinyewa.To sai dai magatardan MDD Kofi Annan,da sakataren harkokin wajen Amurka Colin Powel da ministan harkokin wajen Holland Bernard Bot,dake wakiltan kungiyar EU tare da sergei Lavrov na Rasha,sun hakikance tattauna wannan rikici ,sai dai bazasuyi wa manema labaru bayanin sakamakon taron ba,kamar yadda alada ta tanada.

Sun dai yi ikirarin cewa taron nasu zai haifar da Da mai idanu,dalili kenan dayasa basa bukatar wasu tambayoyi daga yan jarida.

Ministan harkokin wajen Izraela Silvan Shalom,wanda ya gana da Mr Colin Powel saoi kalilan ,bayan shugaba Bush ya gabatar da jawabinsa da baiyiwa Izraelan dadi ba,yace tuni aka sanar dashi cewa kada yaji mamakin batutuwa da zasu fito daga bangarorin hudu.

Daftarin na bukatar hukumar Palasdinu ta kwance damaran yaki,a yayinda Izraela a hannu guda ta dakatar da dukkan harkokinta na matsuggunai a yankin Palasdinu.To sai dai babu alamun cimma wadannan buri,ayayinda batun bawa palasdinu yancin kai a shekara ta 2005,abu ne dake kasa tana dabo,musamman rigingimu dake tashe yanzu a bangaren izraela,dangane matsugunnen yahudawa yan kama wuri zauna,saannan ga batun hare haren kungiyoyin masu tsattsauran raayi na palasdinu kann fararen hula yahudawa.

Idan zaa iya tunawa dai a farkon wannan wata ne prime minista Ariel Sharon yace wannan daftari bazaiyi wani tasiri a bangarensa ba,domin bashi da abokin shawara kann batun sulhu daga bangaren Palasdinu.Adangane da hakane ya zartar da shirinsa na janyewa daga matsugunnai 21 a zirin Gaza,da wasu 4 a arewacin gabar yamma da kogin Jordan,a farkon shekara mai zuwa.

To sai dai ayau Sharon ya sake jaddada gargadinsa wa Mallam Yasser Arafat,inda yake barazar cewa ya tuna da kisan gilla da akayiwa shugabannin Hamas guda biyu a baya.

A hannu guda kuma sabanin yadda kasashe sukayi kunnen uwar shekagu da kiran da Shugaba Bush yayi na gudummowan Dakarun tsaro a Iraki,kasar Poturgal ayau ta bayyana manufarta nacewa ,mai yiwuwa zata bada agajin sojojinta kamar yadda Amurka ta nema a Iraki.Wannan na mai zama martanin wannan kasa ne wa jawabin Shugaban na Amurka da yayi jiya a gaban Majalisar.

Prime ministan Portugal Pedro Santana Lopes yace gwamnatinsa,wadda ke marawa Amurka baya a yakin Iraki,tuni ta tura yansanda kimanin 120 zuwa Irakin ,kuma tana laakari samarda kayayyakin horar da jamian tsaron Irakin.

Mr Kofi Annan wanda a makon daya gabata ya Soki harin na Iraki dacewa baya bisa kaida,ya fadawa Zauren taron cewa dole a dauki akidar darajawa doka ,kuma kada a hana kowa kariya idan yana bukata.

Zainab Mohammed.