1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rana ta hudu ta sauraron shariar Saddam Hussein

Hauwa Abubakar AjejeDecember 6, 2005

Saddam da mukarrabansa 7 ana zarginsu da laifin kashe mutane 148 a 1982,a garin Dujail.

https://p.dw.com/p/Bu3c
Saddam a Kotu
Saddam a KotuHoto: AP

A yau din ma kamar yadda aka fara jiya an kira wasu shaidu da suka bada shaida na irin azabar da suka sha a hannun jamian tsaro a lokacin mulkin Saddam,zargi da Saddam da mukarrabansa su 7 suka karyata.

Shaida ta farko a zaman kotun na yau wata mata ce da aka boye sunanta,wadda kuma tayi Magana ta cikin labule,inda tace an daure tare da azabtar da ita na tsawon shekaru 4 a gidan yari.

A wancan lokaci tace tana yar shekaru 16 ne da haihuwa,a lokacinda jamian tsaron suka tsare ta daga garin Dujail zuwa hedkwatar hukumar leken asiri ta Iraqi kafin a wuce da ita zuwa gidan fursuna na Abu Ghraib.

Matar bata foto fili tace an mata fyade ba,amma tayi ta maimaita cewa an wulakanta ta kuma an keta mata haddi.

Saddam da mutanen 7 da ake zargi suna zaune cikin keji da aka sanya ciki a cikin kotun,suna sauraron wadannan bayanai da shaidun suke bayarwa.

Hakazalika shaida ta biyu a yau din ta bada bayanan yadda aka tsare ta tare da maigidanta da yaransu 7 na tsawon watanni 4 a 1981 tun kafin kashe kashe na Dujail.

Su dai wadannan mata 2 an boye sunayensu da fuskokinsu saboda dalilan tsaro kamar yadda jamian kotun suka baiyana.

Shaida na farko a jiya,Ahmad Hassan dan shekaru 38 ya baiyana yadda aka azabtar da shi da yan uwansa a gidan fursuna dake karkashin Barzan Ibrahim Attikiriti dan uwan Saddam kuma tsohon shugaban hukumar leken asirin Iraqi.

Inda ya rantse cewa ya ga yadda ake nike mutane cikin injin nika,tare da anfani da lantarki ana shockin mutane da harbe gabobinsu a wasu lokuta,nan take kuwa Barzan wanda ke cikin mutanen 7 da ake zargi yayi farat yace karya yake yi,ya kamata a kai shi ya fara wasan kawiwakyo a gidan cinema.

Shi kuma Saddam a lokacinda yake mayarda martani yace, ta yaya wannan shaida wanda yake dan shekaru 15 a wancan lokaci ya san dukkan sunaye da ranakun haihuwar wadanda aka tsare,tare da bada bayanai dalla dalla kamar yadda yayi idan ba kitsa masa su akayi ba.

Daga bisani dai Saddam yacewa alkalin kotun baya tsaron mutuwa kuma yace da shi,idan raina kake so to ka dauka saboda bana tsaron mutuwa.

Lauyoyin Saddam dai tun farko sun ja da halarcin wannan kotu,inda Saddam din shi kansa yace,kotu ce da Amurka ta kafa.

A shariar ta yau ana sa ran shaidu 6 da fito su bada shaidarsu.

Ana dai zargin Saddam da mukarrabansa 7 da laifin kisan gilla na mutane 148 a garin yan Shia na Dujail a 1982 bayan wani yunkuri na kashe Saddam din da akayi,kuma suna fuskantar hukuncin kisa ta hanyar ratayewa idan an tabbatar da wannan laifi a kansu.