1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ranar Aids ta Duniya

Ibrahim SaniDecember 1, 2007
https://p.dw.com/p/CVQo

Yau Asabar rana ce da ta yi dai dai da ranar da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware don yaki da cutar Aids, wato Sida. Ƙasashe daban- daban na duniya na gudanar da bukukuwa don raya wannan rana, musanmamma wajen faɗakar da mutane illolin dake tattare da mugunyar wannan cuta. Shugaba Bush na Amirka ya bayyana cewa, a farko-farkon shekara mai kamawa zai kai ziyara izuwa wasu ƙasashe na Sub Saharan Afrika. Ziyarar a cewar rahotanni za ta mayar da hankaline, wajen yaki da cutar Aids. Mr Bush ya ce Amirka za ta ci gaba da tallafawa ƙasashen na Afrika shawo kan wannan cuta, da a yanzu haka ke barazana ga al´ummar Duniya. Da yawa dai daga cikin ma su ɗauke da wannan cuta sun fitone daga Nahiyar Africa.