1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ranar makoki a kasar Rasha

July 10, 2006
https://p.dw.com/p/BurA

Hukumomin kasar Rasha sun kaddamar da binciken musabbabin hadarin jirgin saman Sibir wanda ya yi sanadiyar mutuwar a kalla mutane 124. Jirgin kirar A-310 wanda ke zurga zurga ta cikin gida daga Mosco zuwa Irkuts ta yankin Siberia ya kasa tsayawa bayan da ya sauka inda ya wuce ya kuma kama da wuta. A kalla mutane 60 wadanda suka sami raunuka su na nan suna karbar magani a asibiti. Da yawa daga cikin fasinjojin da suka rasu kananan yara ne wadanda ke tafiya hutu. Shugaban kasar Rashan Vladimir Putin ya bayana yau litinin a matsayin ranar makoki domin nuna alhini ga mutanen da suka rasa rayukan su.