1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ranar tunawa da kisan kiyashin da aka yiwa Yahudawa

Mohammad Nasiru AwalJanuary 27, 2006

A cikin watan nuwamban bara Majalisar Dinkin Duniya ta ware 27 ga watan janerun kowace shekara don tunawa da ´yantad da sansanin Auschwitz.

https://p.dw.com/p/Bu25
Dandalin tunawa da Yahudawa a Berlin
Dandalin tunawa da Yahudawa a BerlinHoto: AP

Yau dai shekaru 61 ke nan da sojojin TS suka ´yantad da sansanin gwale-gwale na Ausschwitz. Hotunan gawawwaki da tagaiyararru daga wannan sansanin ya ta da hankalin duniya baki daya. To amma mai yasa Jamus ta dauki shekaru 50 sannan gamaiyar kasa da kasa ta kwashe shekaru 60 kafin a ware wata rana ta tunawa da wadanda wannan ta´asa ta rutsa da su? Malamin tarihi na jami´ar Jena Frafesa Norbert Frei ya bayyana ra´ayin sa kamar haka.

“Ina ganin yanzu zamanin wadanda ke da hannu a wannan aikin rashin imani, na dab da gushewa. Sannan sai kuma karin masaniya a tsakanin jama´a akan wannan aika-aika a cikin shekarun baya-bayan nan.”

Hakan kuma na da dangantaka da yadda aka tinkari wannan lamari, inji Edna Brocke, Bayahudiya kuma mai kula da wani tsohon wurin ibadar yahudawa dake birnin Essen, wanda aka mayar da shi karkashin wuraren tarihi na kasa.

“Ina ganin kebe wannan rana yana da muhammanci ga halin da ake ciki a Turai. Wannan nahiya ta zama wani dandalin matsaloli iri dabam-dabam kamar na addini, siyasa da zamantakewa bayan yakin duniya. To amma abin bakin ciki shine an kasa fitowa fili a tinkari wannan kalubale.”

Tambayar da ake yi musamman ma a nan Jamus ita ce wa ke amfana da wannan rana shin wadanda ta´asar ta rutsa da su ko kuma jama´a baki daya? Edna Brocke ta ba da misali da bayanin da wata ta yi ta na mai cewa wannan ta´asa ta ´yan NAZI wani abu ne da bai kamata a ce ya auku ba. To amma da yake hakan ta auku bai kamata a manta da ita ba a yi ta kame-kame sai kace hakan ba ta taba aukuwa ba.

Isra´ila ce ta gabatar da daftarin kudurin kebe wannan rana a gaban MDD kuma ya samu goyon bayan kasashen Larabawa da na musulmi bayan an yi masa ´yar kwaskwarima. Daftarin dai da farko ya tabo maganar nuna kyamar Yahudawa wanda ke barazanar zama ruwan dare a ko-ina cikin duniya. To amma wannan bangare na kudurin bai samu karbuwa a tsakanin mafi ranjaye na membobin MDD ba. Amma duk da haka ana da kyakkyawan fatan cewa kebe wannan rana don tunawa da kisan kiyashin da aka yiwa Yahudawa zai zama mai muhimmanci a nan Jamus da ma a duniya baki daya, musamman saboda masu musanta aukuwar wannan ta´asa kamar irin kungiyoyin nan na masu kyamar yahudawa har da ma wasu gwamnatocin kamar a kasashen Larabawa da na Musulmi, wato kamar shugaban Iran Mahmud Ahmedi Nijad, wanda ke kara yada amnufofin kyamar yahudawa a duniya.

Shi ma Farfesa Norbert Frei na jami´ar birnin Jena ba ya kyautata zaton wannan rana zata taka wata muhimmiyar rawa, to amma ya yi fatan cewa zata zama mai muhimmanci musamman saboda goyon bayan wannan rana da wasu kasashen musulmi suka nuna. Hakazalika zata sa masu adawa da wanzuwar kasar Isra´ila su sake tunani su shiga taitayinsu.