1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ranar tunawa da al'umma ta duniya

Issoufou Mamane /SBJuly 11, 2016

A shekara ta 1989 ne dai kwamitin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ci-gaban kasashe PNUD, ya bukaci tsayar da ranar 11 ga watan Yullin ko wacce shekara a matsyin ranar al'umma ta Duniya.

https://p.dw.com/p/1JNGt
Nigeria Flüchtlingslager Flüchtlinge Kinder
Hoto: DW/S. Ciochina

An kaddamar da wannan rane ce ta al'umma ta duniya baki daya, a wani mataki na janyo hankulan al'umma da ma shugabanni kan muhimmanci da batun al'umma yake da shi ga tafiyar duniya. Taken bikin ranar ta bana dai shi ne: "Zuba jari dan ci-gaban yara mata". Bincike dai ya nunar da cewa, yaran mata a fadin duniya na fuskantar babban kalubale.

Bikin ranar al'umma a Nijar

A wannan shekara ma dai Jamhuriyar Nijar da ke a matsayin wadda ke kan gaba wajen saurin yaduwar al'umma a duniya, ta bi sahun kasashe wajen tunawa da wannan rana ta al'umma. Bincike dai ya nunar cewa, daga mutane milyan 11 a shekara ta 2001, al'ummar ta Nijar ta haura zuwa sama da milyan 17 a shekara ta 2013, yayin da alkaluman binciken kididdiga suka tabbatar da yanzu haka adadin al'ummar kasar ya kai wajen mutun milyan 20. To saidai hukumomin kasar na ganin idan har aka ci gaba da tafiya a haka, to tabbas suna iya fuskantar kalubale a gaba, kamar yadda gwamnan jihar Tahoua Abdourahaman Moussa ke cewa a wani jawabi da ya yi a bikin tunawa da wannan rana ta Al'umma:

Schwangere Frauen in Äthiopien
Hoto: Getty Images

"Yawan haihuwa a gaugauce, na haddasa karin talauci kuma babu shakka wannan ka iya bayyana a fili cewa zai kara yawan wadanda yunwa ke yi wa barazana. Dole ne gwamnatoci su shirya daukar matakai na tsari domin tunkarar matsalar, da kuma warware rayuwar al'umma a yau da ma masu zuwa nan gaba.''

Ko gwamnati ka iya tunkarar kalubalen?

Daga nasu bangare, kungiyoyi irin su UNFPA masu kula da bunkasar al'umma a duniya, na sa shakku ga yunkurin da kasar ta Nijar ke yi duba da hau-hauwan al'ummar da ake gani a cewar Docta Nestor Azandegbe, wakilin na UNFPA a Nijar:

''Kasar Nijar ita ce ke rike da kambun yawan haihuwa a duniya, abun da ke tauye cigaban al'ummar. Gwamnatin kasar za ta iya fuskantar wannan kalubalen? Wannan ita ce tambayar da duk 'yan kasar ya kamata su yi wa kansu.''

Weinendes Kind - Abidjan

Wani bincike da Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar a shekara ta 2012, ya nunar da cewa yawan al'ummar ta Nijar ka iya kai wa miliyan 79, nan da shekara ta 2050 sannan miliyan 209 nan da shekara ta 2100, wannan adadi kuma na iya karuwa idan ya zamana bunkasar al'ummar ta ci gaba a haka ba tare da sassautawa ba.