1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ranar yaki da cutar Aids a dunia

Yahouza SadissouDecember 1, 2005

Yau ne Majalisar Dinkin Dunia ta ware a matsayin rana ta mussaman domin yaki da cutar Aids.

https://p.dw.com/p/Bu3n
Hoto: bzga

Yau ne 1 ga watan desember, ranar da majilasar Dinkin Dunia ta kebe a fadi dunia baki daya, domin fadakarwa da yawo kanan al´umma a game da billa´in cutar Aids kokuma Sida, da ke ci gaba da daukar miliyoyin rayuka.

Rahoton hukumar Majalisar Dinkin Dunia, mai kulla da wannan cuta ,ya sannar cewa fiye da mutane million 40 su ka kamu da kwayoyin ta, daga cikin su million 25 ,sun riga mu gidan gaskiya.

A shekara damu ke ciki, mutane million 3 su ka rasa rayuka sanadiyar cutar kabari sallamu alakaikum.

Idan a ka bi yanki yanki,nahiyar Afrika ce ta hi fama da cutar tare da jimmilar mutane kussan million 26, sannan sai Latine Amurika da kussan million 2.

Kungiyar yaki da cutar, ta yi kira ga kasashe masu hannu da shuni, da kungiyoyin kasa da kasa da su cika alkawuran da su ka dauka, na tallafawa kasashe matalauta, domin su yaki wannan annoba.

A kasashen Afrika mutum daya rak, daga ciki ko wane mutane 10, da ke dauke da kwayoyin cutar, ke samun maganin rage raddadin ta.

Kungiyar na bukatar tattara a kalla dalla billiar 3 da rabi, domin fuskantar yakin a tsawan shekaru 2 masu zuwa.

Wannan lissahi bai shahi ba kudaden da a ke bukata wajen hora da malluman kiwonlahia da kuma daukar dawainiyar yara kanana maruwu sanadiyar cutar.

Kiddidigar da wannan kungiya ta gudanar ta gano cewa a ko wace ranar Allah ta´alla, mutane dubu 14 ke kamuwa da cutar Sida da su ka hada da kanaann yara yan kasa ga shekaru 15 su 2000.

Saidai duk da haka, an dan samu ci gaba a fadi ka tashin da a ke na dakile Aids, ta la´akari da raguwar masu kamuwa da ita a kasashen da ta fi kamari kamar su Kenya da Zimbabwe.

Wani kakakinfadar gwamnatin Amuriak ya yi kira ga kasashen dunia, da su daina daukar sakainan kashi ga cutar Sida, ta hanyar kara yawan kudaden yaki da ita.

Mark Dybul, ya ce a halin da a ke ciki Amurika ke bada kashi daya bisa 2 na yawan kudaden da ake anfani da su a yaki da wannan cuta.

A cewar sa gwamnatin Amurika ta ware zunzuruntun kudade dalla billiar 15, a tsawon shekaru 5, don talafawa kashen Afrika 12 da 2 na Karibien ,su yaki cutar kanjamau.

Ta wannan hanya Amurika ta kashe kussan dalla biliar 3 a sheakara banna.

Ita ma kasar Austriyya ta sannara da bada tallafin dalla million 7 da rabig a kasar India albarkacin wanan ran ata yaki da cuitar Sida.

A jimilce mutane million biyar ne a ka tantance cewar su na dauke da kwayoyin cutar Aids a India, wannan addadi ya jera kasar sahu na 2, bayan Afrika ta Kudu a kasashen da su ka cirri tuta, wajen kamuwa da Aids.

Babban taken da Majalisar Dinkin Dunia ta kebe a shekara bana, albarkacin wannan rana shine mu tashi gaba daya mu tsaida yaduwar cutar Aids a dunia.