1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ranar yaki da yunwa a duniya

Mohammad Nasiru AwalOctober 15, 2004
https://p.dw.com/p/BvfU

Kungiyar ta ba da taimakon abinci ta nan Jamus ta na mai ra´ayin cewa sai da sahihan matakan inganta hanyoyin noma iri dabam-dabam ne kwalliya zata biya kudin sabulu a yakin da ake yi da matsalar karancin abinci da mutane sama da miliyan 840 ke fuskanta a fadin duniya. Domin a halin da yanzu kimanin kashi 70 cikin 100 na mutanen dake fuskantar matsalolin yunwa a kasashe masu tasowa na zaune ne a yankunan karkara, inda suka dogara da irin kayan abincin da suke nomawa a yankunansu. Sakatare-janar na kungiyar taimakon abinci ta Jamus, Hans-Joachim Preuß ya yi suka game da yadda binciken kimiyya ya fi mayar da hankali kan inganta wani nau´in abinci da aka fi nomanshi maimakon binciken ya shafi dukkan abinci da aka sani a duniya, sannan sai ya kara da cewa.

"Ba za´a samu wata nasara ta ku zo ku gani ba, ko da kuwa za´a iya aiwatar da fasahar sauya kwayoyin halittun kayan amfani gona ba da wata matsala ba a kasashe masu tasowa. Alal misali shirin bunkasa aikin noma da aka gabatar a cikin shekarun 1970 bai kai ga kananan manoma a kasashe matalauta ba, saboda haka ban ga yadda sabon shirin fasahar sauya kwayoyin halittun albarkatun noma zai kai ga wannan rukuni na manoma ba. Abu mafi a´ala da za´a yi shine a dauki sahihan matakan inganta aikin noma na gargajiya tare da samar da kyawawan hanyoyin mota da na sadarwa a yankunan karkara."

A bikin ranar yunwa ta bana wanda za´a yi gobe asabar za´a tattauna game da nau´o´in tsirra kimanin dubu 30 da ake da su a duniya da kuma amfaninsu ga shirin samar da abinci a duniya. Yanzu haka dai dubu 7 kadai na irin wadannan tsirrai ne ake amfani da su a matsayin abinci, inji Matthias Berninger sakatare kasa a ma´aikatar harkokin noma ta tarayyar Jamus. A saboda haka nan gaba duk wani taimakon raya kasa da Jamus zata bayar zai ta´allaka akan inganta aikin noma a yankunan karkara na kasashe masu tasowa. Sakatare ya ce yunwa ba matsala ce ta fasaha da za´a iya magance ta ta hanyar noman hatsi kamar masara, alkama shinkafa ko soya da aka sauya masu kwayoyin halittu ba. Sakatare ya kara da cewa dole ne a mayar da hankali akan noman kayan abinci da aka fi amfani da su tun zamanin kakannin kaka. Wani muhimmin abu kuma shine fadada kasuwanni a kasashe masu tasowa. A dangane da haka mista Berninger ya yi nuni da cewa dole ne kasashe masu ci-gaban masana´antu su kara rage kudaden tallafi da suke bawa manomansu kana kuma su daina sayarwa ko kuma tura rarar albarkatun nomansu a matsayin taimakon abinci ga kasashe masu karamin karfi.