1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ranar yan Jarida ta duniya

May 3, 2007
https://p.dw.com/p/BuMK

Yau a ko ina a faɗin duniya ake bikin ranar yancin yan jarida. Sai dai a wani bincike da kwamitin kare haƙƙin yan jarida na ƙasa da ƙasa ya gudanar, ya yi nuni da cewa tauye hakkin yan jarida ya yi tsammari matuƙa a wasu sassan ƙasashe na duniya. Rahoton yace an sami koma baya ga yancin yan jarida na gudanar da ayyukan su kamar yadda ya kamata. Yace gwamnatoci na amfani da wasu tsauraran dokoki domin yiwa aikin yan jarida tarnaki. Rahoton ya baiyana ƙasashen Morocco da Thailand a matsayin ƙasashe waɗanda shekaru biyar da suka wuce suka zamo abin misali wajen kare haƙƙin yan jarida, amma kuma a yanzu suka bata rawar su da tsalle ta kafa dokoki da suke wa aikin jarida zagon ƙasa. Sauran ƙasashe da rahoton ya ambata dake tauye haƙƙin yan jarida sun haɗa da Azerbaijan da Masar da Pakistan da Cuba da jamhuriyar dimokradiyar Kongo da Rasha da Gambia da kuma ƙasar Habasha.