1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rangadin cibiyoyin nukiliyar Jamus

August 18, 2010

Shugabar gwamnatin Jamus ta fara rangadin cibiyoyin makamashin nukiliyar ƙasar - a ƙoƙarin sake fasalin su

https://p.dw.com/p/OqE2
Hoto: AP

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta fara rangadin yini huɗu a cibiyoyin samar da makamashi da ke sassa daban daban na Jamus. Za ta ziyarci cibiyoyi 10 ne da suka haɗa da na gawayin kwal da na niukiliya da kuma makamashin da ake samar wa ta hanyar Iska.

Wannan rangadin na zuwa ne kwanaki ƙalilan - gabannin gwamnati ta bayyana wata sabuwar manufa ce da ta shafi batun makamashi a makon da ke tafe - idan Allah ya kaimu. Sabuwar manufar dai na da nufin inganta dokokin makamashi ne ga hanyoyi daban - daban na samar da makamashin.

Akwai yiwuwar sabuwar manufar ta tsawaita wa'adin yin amfani da cibiyoyin niukiliya ta yadda zai zarta wa'adin shekara ta 2020 da tunda farko aka yi na'am da shi a ƙarƙashin tsohuwar ƙawancen jam'iyyun Greens da kuma ta Social Democrat. Gwamnatin Jamus da ke mulki a yanzu na da ra'ayin cewar, yin amfani da niukiliya ce ya fi dacewa gabannin samar da sabuwar fasahar yin amfani da iska da kuma ruwa domin samar da makamashin.

Ana samun rarrabuwar kawuna a tsakanin Jamusawa bisa batun makamashin niukiliya, inda ƙiyasi ke nuna cewar fiye da rabin al'ummar ƙasar ne ke nuna goyon bayan su ga ɗaukar matakan rufe cibiyoyin.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu