1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rangadin Codoleesa Rice a gabas ta tsakiya

October 16, 2007
https://p.dw.com/p/Bu8K

Sakatariyar harakokin wajen Amurika Condoleesa Rice, na ci gaba da rangadi a yankin gabas ta tsakiya, a yunƙurin neman bakin zaren warware rikicin wannan yanki.

A yayin ganawar ta da hukumomin Isra´ila da na Palestinu, ta bukaci su cimma daidaito, akan manufa ɗaya, wadda za a gabatar ga taron ƙolin da Amurika ke buƙatar shiryawa a wata mai kamawa.

Wannan taro zai hada banagarori daban daban masu hanu a cikin rikicin, da zumar cimma tudun dafawa.

A cewar Condolesa Rice, lokaci yayi na girka cikkakar ƙasa ta Palestinu, wace zata gudanar da mu´amila cikin girma da arziki tare da maƙwabciyar ta, Isra´ila.

Nan gaba a yau, Condolesa Rice, zata je Masar, inda zata gana da shugaba Osni Mubarak.

Za ta ci gaba da wannan rangadi har ranar alhamis mai zuwa.