1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rangadin Shugaban Brazil a yankin Afirka

July 7, 2010

Shugaban Tanzania ya ce ƙasar sa za ta ci gajiyar hulɗa da Brazil musamman ta fuskar fasaha

https://p.dw.com/p/ODb0
Hoto: AP

A ci gaba da rangadin da yake yi a nahiyar Afirka, shugaban ƙasar Barazil Luis Inacio Lula da Silva ya isa ƙasar Tanzania inda ya halarci kasuwar baje kolin kayayyakin kasuwanci a Dar - es - Salam, babban birnin ƙasar Tanzania. Shugaba Jakaya Kikwete na ƙasar Tanzania ne ya rufa wa Shugaban na Brazil baya a lokacin da yake zagayawa a runfunan da aka baje kayayyakin, inda ya ce Tanzania na da abubuwa da dama da za ta ci gajiyar su daga haɗin kai da ƙasar Brazil. Shugaba Kikweti ya ƙara da cewar:

" Mu, a ƙasar Tanzania zamu ci gajiya sosai daga kusanci da kuma haɗin kai da ƙasar Brazil. Muna neman kasuwannin da za mu sayar da hajojin mu. Idan har muka yi nasarar shiga cikin kasuwannin Brazil, to kuwa zamu yi farin ciki sosai domin bunƙasa ƙasar mu. A matsayin ta na ƙasar dake da jarin da za ta saka a wasu ƙasashen duniya, Brazil tana da ƙwarewa ta fannin fasaha, kuma mu a Tanzania muna matuƙar buƙatar fasaha domin taimakawa ci gaban ƙasar mu."

Gabannin saukar shugaba Lula da Silva a Tanzania dai, sai da ya yada zango a ƙasar Kenya inda ya yi alƙawarin tallafa mata a fannin Noma.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Ahmad Tijani Lawal