1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rangadin Tony Blair a Afrika

May 30, 2007
https://p.dw.com/p/BuKE

Praministan Britania Tony Blair, na cigaba da rangadin ban kwana, a nahiyar Afrika.

Bayan ƙasar Lybia da ya ziyarta jiya, a yau ya yada zango a ƙasar Liberia, inda zai gana da shugaba Ellen Searleaf Johson, a game da mu´amilar cinikaya da diplomatia tsakanin Liberia da Britania.

A matakin farko na wannan rangadi, tawagogin Britania da na Lybia, sun rattaba hannu a kann yarjeniyoyi daban-daban, ta fannin tsaro da kasuwanci.

A ɓangaren tsaro, yarjejeniyar ta ba Lybia, damar sayen makamai masu lizzami daga Britania, da kuma hora da sojojin Lybia.

A ɗaya gefen, Lybia ta ba kampanin haƙar mai na Britania, wato BP, kwangilar dalla milion 900, ta fannin binciko Gaz a cikinsahara.

Tun shekara ta 1999, a ka sake ƙulla hulɗoɗin diplomatia, tsakanin Britaia da Lybia, bayan hukumominTripolie, sun damƙawa London, mutanen nan 2, da ake tuhuma da hannu a harin ta´adancin da ya rutsa da jirgin sama samparin Pan Am, a ƙasar Britania, wanda kuma ya yi sanadiyar mutuwar mutane 270, a shekara ta 1988.