1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rangadin Wen Jiabao a nahiyar Afrika

June 19, 2006
https://p.dw.com/p/ButI

Praministan ƙasar Sin, Wen Jiabao na ci gaba da rangadin kwanaki 7 a nahiyar Afrika.

Bayan Masar, jiya, ya sauka Accra babban birnin ƙasar Ghana, inda ya gana da shugaban ƙasa John Kuffor.

A yayin da ya ke bayyani ga maneman labarai, Wen Jiabao ya kyauttata zaton, ƙara danƙon cuɗaya, tsakanin ƙasashen 2, mussamman ta fannin harakokin saye da sayarwa.

A halin da ake ciki, ƙasar China, ta mamaye kasuwannin nahiyar Afrika, tio saidai a cewar hukumomin Bejing, wannan hulɗoɗi na buƙatar gyara.

Tunni, Ghana da Sin, sun cimma yarjejeniyar, ta fannin harakokin sadarwa, kazalika Sin, ta alkawarta aika tawagar ƙurrarun likitoci, zuwa Ghana, da kuma agaji ta fannin zuzrfafa illimi a jami´o in ƙasar.

Ƙiddidigar da masana harakokin tattalin arziki na ƙasashen 2 su ka gudanar, ta gano cewar, hulɗoɗin kasuwanci tsakanin su, sun lunka har sau 10, a tsawan shekaru 10 da su ka gabata.

Daga dalla million 76 a shekara ta 1995, kudaɗen cinaki a tsakain su sun kai dalla millions 760 a shekara ta 2005.

Nan gaba a yau ,Wen Jiabao, sai tashi daga Ghana, zuwa Angola, sannan zai ziyarci Jamhuriya Demokradiyar Kongo, Afrika ta kudu, Tanzania da Uganda.