1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rantsar da gwamnatin Iraki a karo na biyu

Zainab A MohammadMay 9, 2005

Rikici na cigaba da addaban Iraki,adaidai lokacin da sabuwar gwamnati ke neman gindin zama

https://p.dw.com/p/Bvc5
Hoto: AP

A yau ne aka sake rantsar da sabuwar gwamnatin Iraki a karo na biyu cikin tsukin mako guda,dangane da matsin lamban shugabannin kurdawan kasar na mayar da kaidoji irin na mulkin hadaddiyar kasa,wanda aka cire daga cikin ainihin takardar ransuwa da akayi amfani dashi a ranar 3 ga wata wajen rantsar da Prime Ministan da ayayirin ministocinsa.

Prime minister Ibrahim Jaafari,shine mutumin farko da aka rantsar inda ya dafe hannunsa kan littafi mai tsarki,watau Alkurani.Ministar kimiyya da fasaha Bassema Yusef Butrus,wadda ke kasancewa Krista guda,daga cikin ministoci 36 na Irakin,tayi rantsuwar yiwa Iraki aiki cikin gaskiya da adalci dafe da hannunta kan takardar Bible.

Dukkan Ministocin da aka rantsar ayau dai sunyi alkawarin sauke nauyi daya rataya a wuyansu na darajawa yancin Iraki,da aiki wa alummar kasar,da kare mutuncinta da dumbin albarkatun ruwa dana kasa da Allah ya huwace mata, tare kuma da tabbatar da tafarkin democradiyya,cikin adalci da gaskiya.

An cire bangaren da aka ambata hadaddiyar kasar Iraki acikin takardar rantsuwa da akayi amfani dashi a makon daya gabata wajen rantsar da sabuwar gwamnatin,batu da shugabbanin kurdawa suka yi adawa dashi.A ranar jummaa nedai shugaban jammiyyar Kurdawa Massoud Barzani,yayi gargadin cewa cire wannan batu a cikin takardar rantsar da shugabannin zai yi barazanar hadewan kurdawa day an darikar Shia a majalisar mulkin Iraki.

Jammiyyar hadin gwiwa ta yan darikar shia wanda Ibrahim Jaafari kewa jagoranci ,itake rike da fiye da rabin kujeru a majalisar dokokin kasar,amma na bukatar goyon bayan yan majalisar Kurdawa guda 77,domin samun rinjayen zartar da kowane batu dake da muhimmanci a majalisar.

Wannan tsari na haddadiyar kasa dai nada muhimmanci wa kurdawan Iraki,wadanda keda rinjaye da kuma daukaka a arewaci,kana ke neman tabbabar dashi cikin kundun tsarin mulkin Irakin,da ake shirin rubutawa cikin wannan shekara.

To sai dai hausawa nacewa bukin magaji baya hana na magajiya,domin kuwa ayayinda ake bukin rantsar da gwamnatin Iraki a karo na biyu,akalla mutane 7 suka rasa rayukansu a yau a Irakin ,wadanda suka hadar da yansanda biyu,da shugaban jamiin tsaro dake jagorantar rundunar dake tsaron naurorin man petur,ayayinda yan yakin sunkurun kasar ke cigaba da kai hare hare sassa daban daban.

Wasu yan Irakin hudu sun rasa rayukansu banda wasu 8 da suka jikkata,lokacin da wani dan kunar bakin wake ya afkawa motocin yansanda biyu da motarsa dauke da boma bomaia yankin kudu maso yammacin Bagadaza.Nan take Jamian yansanda biyu suka kone kurmus cikin motocinsu.

Bugu da kari Lt. Col.Omar Dalaf al-Qaissy dake jagorantar dakarun tsaro dake matatar mai dake garin Baiji ,mai tazarar km 200 arewacin Bagadaza ya gamu da ajalinsa,lokacinda wasu yan bindiga dadi suka tsayar da motarsa akan hanyarsa zuwa gida daga office.Jamian tsaro sun sanar da samun gawansa dauke da harsashai guda 22.

Kazalika a arewacin Iraki wasu yan yakin Sunkuru sun bindige Sami Nazar Ali ,matukin babbar mota,a harin da aka afkawa dakarun Amurka dake garin Ishaki.Bugu da kari Bomb ya tarwatse a daidai lokacin da ayarin hadin gwiwa na dakarun Amurka da Iraki ke wucewa cikin kauyen Shabab,dake wajen Bagadaza,harin daya ritsa da ran sojin Iraki guda.

A hannu guda kuma Dakarun amurka sun kaddamar da hari a gunduwar Anbar dake yammaci sakamakon sabbin hare hare dake kasancewa barazana wa wannan sabuwar gwamnati dake neman gindin zama.Rahotanni ya zuwa yanzu dai na nuni dacewa Dakarun Amurkan sun kasha akalla mutane 75,wadanda injisu yan yakin sari ka noke ne.