1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rantsar da sabuwar Shugabar Liberia

Hauwa Abubakar AjejeJanuary 16, 2006

Shugabannin kasashen Afrika da manyan jamian kasashen duniya suka halarci bikin rantsar da sabuwar shugabar kasar Liberia,Ellen Johnson a yau,mace ta farko zababbiyar shugaba a Afrika.

https://p.dw.com/p/Bu2Q
Ellen Johnson Sir-Leaf
Ellen Johnson Sir-LeafHoto: AP

Cikin wadanda suka halarci bikin rantsar da Ellen Johnson Sir-Leaf, yau, har da uwargidar shugaba Bush na Amurka,Laura Bush,da sakatariyar harkokin wajen Amurka Condolezza rice,wadanda ake ganin kasancewarsu wajen bikin, wata alama ce ta irin goyon baya mai karfi da Amurka take baiwa Ellen Johnson,wadda tayi alkawarin farfado da kasar da yaki ya tagaiyara.

Ellen yar shekaru 67 da haihuwa,tsohuwar ministar kudi ta kasar,ta kada tsohon dan wasan kwallon kafa kuma miloniya George Weah a zaben shugaban kasa na watan nuwamba.

Yan kasar ta Liberia dai da yaki ya lallasa,sun dora dukkanin fatarsu akan,sabuwar shugabar wadda suke kira Mama Ellen,da kuma Amurka da suke ganin uwargijiyace a garesu.

Kasar Liberia,mai yanci mafi dadewa a Afrika,yantattun bayin Amurka ne suka kafa ta a 1847 kuma har yanzu dangantaka tsakanin Amurka da Liberia sai kara zurfi takeyi.

An ji daga bakin wani dan tireda Ben Sackor yana fadin cewa,ya kamata Amurkan ta taimaka sake gina Liberia,saboda a cewarsa har yanzu suna cikin duhu na rashin hasken wutar lantarki shekaru 15 ke nan,yace hakki ne akan Amurka ta taimakawa kasarsa.

Jamain Amurka dai sunce,gwamnati ta kashe fiye da dala miliyan 840 a shekarar da ta gabata akan kasar Liberia,yayinda take farfadowa daga yakin basasa da yayi sanadiyar rayukan mutane akalla 250,000 tare da lalata kasar baki daya.

Jamian na Amurka sunce,taimakawa Liberia yana daya daga cikin muhimman abubuwa da gwamnatin Bush ta sanya a gaba,amma talakawan Liberia suna bukatar Amurka ta farfado da wutar lantarki da samarda ruwan sha,gina asibitoci da makarantu,tare da horasda alkalai da sabbin sojojin kasar.

Manyan jiragen yakin ruwa na Amurka guda 2 aka girke gadi,yayinda Laura Bush,Rice da shugabannin Afirka da sauran manyan jamiai na sauran kasashen duniya suke halartar wannan biki.

Jamian leken asiri na Amurka sun shige cikin dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a babban birnin kasar Monrovia,inda aka kwashe dukkan datti,aka like tare da fenti ga gine gine da harsasai suka lalata domin wannan biki.

A halin yanzu dai kasar Sin wadda take rigengeniya da Amurka,wajen tabo albarkatun mai na Afrika,ita ma tana kokarin karfafa dangantaka da Ellen Johnson ta Liberia.

Domin kuwa a yanzu haka ministan harkokin wajen Sin, Li Zhaoxing wanda ke rangadin kasashen Afrika 6,yana Liberia wadda tun jiya suka gana da sabuwar shugabar,inda ya baiyanawa manema labarai cewa,kasar Sin da Liberia suna da raayi guda akan batutuwa da dama,kamar sake yiwa MDD gyaran fuska.

Ya kuma yi tayin taimakon Liberia ta fannin sake gina filayen wasanni,aikin gona da horas da matasa.

Masu lura da almaura sunce alwashin da Johnson ta sha,na yaki da cin hanci da tabbatar da zaman lafiya a Liberia,ba zai samu ba,sai dai idan masu bada gudumowa na kasa da kasa,kamar Amurka sun cika alkawuran da suka dauka na taimaka mata.