1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rantsar yan majalisar Afganistan

Zainab A MohammadDecember 19, 2005
https://p.dw.com/p/Bu7l

AFGANISTAN

Shugaba Hamid Karzai na afganistan na laakari da yiwa majalisar ministocinsa garon bawul,tare da rage yawan ministocin ,bayan ya rantsar da yan masjalisar dokoki na farko a wannan kasa cikin shekaru da dama.

Majalisar dokokin da aka rantsar yau dai nada ikon amincewa da ministocin da Karzai zai zaba,mutumin aka rantsar dashi a matsayin zababben shugaba na farko a Afganistan a bara.

Sanarwa daga fadar gwamnati dake kabul nas nuni dacewa gyare gyaren zai hadar da manyan maaikatun kasar da suka hadar dana harekokin waje .Bugu da kari zaa rage yawan ministocin ta hanyar hade maaikatu guda biyu a karkashin minista guda.Ministan tsaron Afganistan Abdul Rahim Wardak ya tabbatarwa manema labaru wannan shiri na gwamnati,ba tare da wani karin bayani ba.

A yanzu haka dai Afganistan nada Maaikatu 27,akarkashin jagorancin ministoci daban daban da suka hadar da tsofin jamian soji da mata.

Yan kasar dai sun koka dacewa akasarin ministocin basu da kwarewa,domin sun samu mukaman ne saboda siyasa,a kokarin da shugaba Karzai keyi na hade kann kungiyoyin dake gaba da juna,da yan adawa.