1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rarrabuwar kai a tsakanin 'yan Najeriya

Al-Amin Suleiman Muhammad/YBSeptember 5, 2016

Wani sabon rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, ya nunar da cewa akwai rarrabuwar kai tsakanin bangarorin al’ummar kasar, inda banbancin kabila da addini da kuma yanki ya maye gurbin kishin kasa.

https://p.dw.com/p/1JwA4
Unabhängigkeitstag in Nigeria 2015
Lokutan bukukuwa dai akan ga 'yan Najeriya na hada kai a yi biki tareHoto: Reuters/A. Akinleye

Rahoton da ake kira Common Country Analysis (CCA) ya nuna cewa kananan kabilu da kuma yankuna na yin korafin rashin yi musu adalici da babakere a harkokin gwamnati da rabon mukamai. Rahoton ya kuma nuna cewa akwai tsananin yunwa inda kashi 10 cikin 100 na yara ne kacal ke samun abincin da ya kamata a kasar da ake hasashen yawan al'ummar ta zai kai miliyan 200 zuwa shekara ta 2019.


Bangarorin ‘yan Najeriya sun gaskata wannan rahoto wanda suka ce shi ne hakikanin yanayin da kasar ta ke ciki, inda bangaranci da kabilanci da kuma addinanci da ma kungiyanci ke juya rayuwar daukacin al'ummar kasar.

Nigeria Ramadan
Bushe-bushe na zama wata alama ta wasu kabilu a NajeriyaHoto: picture-alliance/AP Photo/G. Osodi


Masharhanta dai na bayyana dalilai na samun rarrabuwar kai tsakanin al'umma wanda ke barazana ga zamantakewa tsakanin kabilu daban-daban da ke haifar da rikicin addini da kabilanci. A cewar Salihu Abdullahi mai littafi wani mawallafi, tun juyin mulkin da aka yi a shekarar ta 1966 wanda aka hallaka wasu shugabannin shiyoyin kasar aka yi barin hadin kan da shugabannin da suka karbo mulki Najeriyar suka samar.