1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha na binciken harin Bom na kasar

April 3, 2017

Mahukuntan kasar Rasha sun sha alwashin gano tushin harin birnin tasahoshin jiragen kasa da ya halaka rayukan jama'a.

https://p.dw.com/p/2abv7
Russland Präsident Putin in Sankt Petersburg
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Metzel

Hukumar binciken manyan laifuka a kasar Rasha ta fara binciken harin Bom na birnin St. Petersburg wanda aka danganta da hari na ta'addanci.

Hukumar wadda ke da karfi a kasar ta ce tuni ta aike da jami'an bincike, don tono duk wasu bayanai kan harin na Bom da ya shafi tashoshin jiragen karkashin kasa biyu a birnin inda akalla mutane goma suka salwanta.

Harin dai ya faru ne yayin da Shugaba Vladimir Putin ke ganawa da shugaban kasar Belarus a birnin na St. Petersburg.

Bayanai sun ce an ma sami wata nakiyar a wata tashar, sai dai bata fashe ba.

Akaluman wadanda suka jikkata ma dai sun kai kimanin mutane 50, wadanda ke fama da munanan raunuka.

Tuni dai hukumomin kasar Jamus da Amirka suka yi Allah wadai da harin na Rasha a wannan Litinin.