1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta ce za ta ci gaba da sayar wa Iran makamai.

November 17, 2006
https://p.dw.com/p/BubR

Rasha ta ce tana ci gaba da cika ƙa’idodjin yarjejeniyar da ta cim ma da Iran wajen sayar mata makaman zamani na kariya da hare-haren jiragen sama da rokoki. Ma’aikatar tsaron Rashan ne ta bayyana haka yau a birnin Moscow, a wani matakin da ake gani kamar mai da martani ne ga kiran da Amirka ta yi mata na ta sake tunani kan sayar wa Iran ɗin waɗannan makaman. Da yake amsa tambayar maneman labarai, shugaban hukumar ma’ammala da fasahar kayayyakin soji ta ƙasar Rashan, Mikhail Dmitrev, ya ce ko me na tafiya daidai kamar yadda yarjejeniyar da suka ƙulla da Iran ta tanadar. Kuma za su cika duk ƙa’idojin da kuma duk wani alkawarin da suka ɗauka. Babu dai wani dalilin sake yin wani tunani kann aiwatad da yarjejeniyar, inji Dmitrev

A cikin watan Agustan da ya gabata ne dai, Amirka ta ba da sanarwar sanya wa wasu kamfanonin Rasha takunkumi, saboda sayar wa Iran wasu kayayyakin da take gani, za ta iya yin amfani da su wajen sarrafa makaman ƙare dangi.