1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta fara janye dakaru daga Siriya

Suleiman BabayoMarch 15, 2016

Rasha ta fara tabbatar da matakin da ta yi alkawari na janye dakaru daga kasar Siriya mai fama da tashe-tashen hankula da ke da nasaba da siyasa.

https://p.dw.com/p/1IDXB
Syrien russische Kampfjets
Hoto: picture alliance/dpa/Russian Defence Ministry

A wannan Talata rukunin jiragen sama na farko na Rasha sun fice daga kasar Siriya, matakin da ake gani zai karfafa zaman tattaunawa da Majalisar Dinkin Duniya ke jagoranta. Haka ya zo kwana guda bayan sanarwar da Shugaba Vladimir Putin na kasar ta Rasha ya bayar na janye wasu dakaru daga cikin kasar ta Siriya mai fama da tashe-tashen hankula.

Manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniya kan rikicin Siriya Staffan de Mistura ya bayyana janyewar da Rasha ta fara daga Siriya a matsayin wani muhimmin mataki. 'Yan adawa na kasar ta Siriya suna cikin wadanda suka yi maraba da matakin na Rasha.