1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta janye daga yarjejeniyar dakarun turai

November 30, 2007
https://p.dw.com/p/CVBf

Shugaban Rasha Vladmir Putin ya sanya hannu kann wata doka ta janyewar Rasha daga wata yarjeneiya ta kafa rundunar haɗin kai a turai da ake ganin muhimmi ne ga tsaron nahiyar.Yarjejeniyar ta 1999 ta ƙayyade yawan manyan makamai da za a girke a tsakanin tekun Atlantica da tsaunaukan Urals.Wannan doka da Putin ya sanyawa hannu ya nuna cewa nan gaba Rasha ba zata sake amincewa rundunar tsaro ta NATO yin bincike a gurarenta na soji ba.Gwamnatin Rasha tace ta ɗauki wannan mataki ne don nuna adawa da shirin Amurka na kafa tashar kariya ga makamai masu linzami a kasar Poland da Jamhuriyar Czech.Wannan sanarwar ta zo ne `yan kwanaki kaɗan kafin zaɓen majalisar dokoki ta Rasha.

A halinda ake ciki kuma ƙungiyar ta NATO ta roƙi Rasha da kada ta yi zagon ƙasa ga wannan muhimmiyar yarjejeniya da aka kafa tun zamanin tsohuwar Taraiyar Soviet.