1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Rasha ta sake kai hare-hare kan tashoshin makashi a Ukraine

March 30, 2024

Ukraine ta nuna bacin ranta dangane da sabbin hare-haren da dakarun Rasha suka kaddamar a kan tashonshinta da ke samar da hasken wutar lantarki. Lamarin ya haddasa daukewar wuta a wasu yankuna.

https://p.dw.com/p/4eGhR
Yadda ake fama da duhu a wani yanki na Ukraine
Yadda ake fama da duhu saboda daukewar wuta a wani yanki na UkraineHoto: picture alliance / AA

Wasu yankunan kasar Ukraine uku, sun fuskanci daukewar wutar lantarki bayan hare-hare da dakarun Rasha suka kai kan wasu tashoshin samar da wutar a jiya Juma'a.

Hukumomi a Ukraine sun ce akwai hari na makami mai linzami da kuma na wani da aka kai da jirage marasa matuka a kan tashohi da dama wadanda ke samar da makamashin na lantarki.

Daga ciki har da wasu tashoshi na dam-dam da wadanda ke amfani da tururi.

A baya dai Shugaba Volodymyr Zelenskyy na kasar Ukraine ya kwatanta hare-haren Rasha kan cibiyoyin samar da wutar lantarki a matsayin wani ''ta'addanci na makamashi.''

Jakadan Amurka a Ukraine din ma ya yi Allah wadai da hare-haren da Rasha ke kaiwa a kan cibiyoyin na lantarki da miliyoyin mutane suka dogara a kansu.