1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta yi kashedi ga Iran game da shirin ta Nukiliya.

Tanko Bala, AbdullahiFebruary 27, 2008

Gwamnatin kasar Rasha tace zata goyi bayan karin takunkumi akan Iran idan ta ki dakatar da bunkasa sinadarin Uranium

https://p.dw.com/p/DEYn
Jamíi a daya daga cikin tashoshin Nukiliyar IranHoto: AP

Jakadan kasar Rasha a Majalisar Ɗinkin Duniya Vitaly Churkin wanda ya sanar da hakan ga yan jarida a birnin New York, yace idan har nan da yan kwanaki kadan, Iran taki dakatar da bunkasa sinadarin na Uranium, to labudda zata goyi bayan sabon daftarin takunkumin da kasashen yammacin Turai za su gabatarwa kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya a wannan makon domin kara mayar da ita saniyar ware.

Kasashen Amirka da Britaniya da Faransa da kuma Jamus na cigaba da matsa kaimi don amincewa da sabon daftarin takunkumi akan Iran wadda suke zargi na yunkurin kera makamin kare dangi a asirce. Kwamitin sulhun majalisar Dinkin Duniyar ya bukaci Iran ta dakatar da bunkasa sinadarin na Uranium wanda kasashen na yammacin ke baiyana damuwa cewa ana iya amfani da shi wajen kera makamin Atom.

Tuni kasashen Faransa da Britaniya suka gabatar da daftari na uku na takunkumin wanda suke fatan kakabawa Iran. Matakan sun kunshi rike kadarorin gwamnatin da haramtawa shugabanin kasar tafiye tafiye zuwa kasashen Turai. Bugu da kari kasashen na Turai sun kuma fadada jadawalin sunayen jamiái da kamfanonin Iran din da takunkumin zai shafa. Matakai biyu na farko na takunkumin Majalisar Dinkin Duniyar da aka sanyawa Iran an yi su a watan Disamba na shekarar 2006 da kuma watan Maris na shekarar 2007. A wancan lokaci Rasha wadda ke da kwakwarar hukldar dangantaka da Iran ta yi ta nuna dari-dari wajen amincewa a sanyawa Iran din takunkumin karya tattalin arziki.

Babban jamiín harkokin wajen kungiyar tarayyar Turai Javier Solana ya tabbatar da matsayin kasar Rasha na bada goyon baya ga sanyawa Iran karin sabbin takunkumi. Shi ma Ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeier a ziyarar da yake yi a nahiyar Asia, ya yi kira ga Indonesia a matsayin ta na babbar kasar Muslimi ta ja hankalin mahukuntan Iran wajen dakatar da bunkasa makamashin na Uranium.