1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta yi wa 'yan tawayen Siriya tayin ficewa daga Alepo

Gazali Abdou Tasawa
October 13, 2016

A daidai lokacin da jiragen yakin gwamnatin Siriya da na Rasha ke ci gaba da lugudan wuta kan birnin Alepo, kasar Rasha ta ce a shirye take ta bayar da kariya ga mayakan 'yan tawayen da ke bukatar ficewa daga birnin. 

https://p.dw.com/p/2RCcY
Syrien Krieg - Zerstörung in Aleppo
Hoto: Reuters/A. Ismail

A kasar Siriya a daidai lokacin da jiragen yakin gwamnatin kasar da na Rasha ke ci gaba da lugudan wuta kan birnin Alepo, kasar Rasha ta ce a shirye take ta bayar da kareya ga mayakan 'yan tawayen da ke bukatar ficewa daga birnin. 

Janar Serguei Roudskoi daya daga cikin shugabannin sojojin rashar ne dai ya sanar da hakan a wannan Alhamis inda ya ce a shirye  kuma amince da ficewar fararan hula daga yankin gabashin Alepo dama shigar da kayan agaji a cikin unguwannin 'yan tawayen wadanda sojojin Bachar al-Assad ke kokarin maido da su a karkashin ikonsu. 

Wanan tayi na kasar Rasha ya zo a daidai lokacin da kasashen Amirka da Rasha ke shirin gudanar da wasu taruka  tare da hadin gwiwar kasashen Larabawa  da na Turai a biranen Lusanne da London  a karshen mako da nufin sake cimma wata yarjejeniyar tsagaita wuta a birnin na Alepo