1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta zargi ƙasar Georgia da gudanad da ayyukan ta’addanci.

October 1, 2006
https://p.dw.com/p/Buhl

Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya nuna matuƙar ɓacin ransa ga rikicin diplomasiyyan da ya ɓarke a halin yanzu a ƙasar Georgia. Ya ce kame hafsoshin Rashan guda 4 da jami’an Georgian suka yi a ran larabar da ta wuce, saboda zargin da suke yi musu na leƙen asiri, wato gudanad da ayyukan ta’addanci da kuma yin garkuwa da mutane ne da mahukuntan ƙasar gaba ɗaya ke yi. A jiya asabar ne dai Rashan ta janye duk jami’an diplomasiyyanta daga ƙasar ta Georgia.