1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin tabbas ga zaɓe a Gini

October 28, 2010

An sake ɗage ranar gudanar da zaɓen ƙasar Gini dake yammacin Afirka

https://p.dw.com/p/PrHg
Yaushe al'ummar ƙasar Gini za su sake samun wannan dama ta kaɗa ƙuri'a?Hoto: picture alliance/dpa

Hukumomi a ƙasar Gini sun ba da sanarwar sake ɗage ranar gudanar da zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasar da aka shirya gudanarwa a ranar Lahadi mai zuwa. Yanzu haka dai an tsayar da ranar 7 ga watan Nuwamba a matsayin ranar gudanar da zaɓe. Da yammacin jiya shugaban riƙon ƙwarya Janar Sekouba Konate ya fid da wata doka wadda ta tabbatar da sabon lokacin yin zaɓen. A zagaye na farko na zaɓen da ya gudana a ƙarshen watan Yuni, tsohon Firaminista Cellou Dalein Diallo da mai ƙalubalantarsa Alpha Condé suka tsallake siraɗi zuwa zagaye na biyu. Da farko an shirya gudanar da zaɓen a ranar 18 ga watan Yuli, amma aka ɗage.

A wani labarin kuma ɗan takarar shugaban ƙasar Alpha Condé ya janye daga wani rangadin haɗin guiwa na neman zaman lafiya da za su yi yau Alhamis da abokin hamaiyarsa Cellou Dalein Diallo, da cewa magoya bayansa na adawa da rangadin. Kakakin ƙawancen jam'iyun Rainbow masu goyon bayan Condé, ya ce Farfesa ya yi niyar shiga rangadin na haɗin guiwa amma masu ma'amala da shi ba sa so. Da farko dai an shirya 'yan takarar neman shugabancin ƙasar su biyu da wata tawagar wakilan gwamnati da na addini za su yi rangadi faɗakarwa a yankunan da rigingimun siyasa da na ƙabilanci suka auku gabanin wannan zaɓen.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Umaru Aliyu