1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin tabbas game da zaɓen Gini

Zainab MohammedSeptember 13, 2010

Hukumomin Gini Conakry sun dakatar da yaƙin neman zaɓe sakamakon tashe-tashen hankula da ake fiskanta tsakanin magoya bayan 'yan takara biyu.

https://p.dw.com/p/PAyU
Gangamin siyasa a GiniHoto: AP

A Gini Conakry, tashe-tashen hankula da suka wakana a ƙarshen mako sun fara haifar da shakku game da yiwuwar gudanar da zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasa. Hukumomin Conakry sun dakatar da yaƙin neman zaɓe sakamakon mutuwar mutun ɗaya da kuma jikata mutane 50 da aka yi a fito na fito tsakanin magoya bayan 'yan takaran biyu a ranar lahadi.

A halin da ake cikin yanzu dai, 'yan takara biyu da za su ƙalubalancin junansu a zaɓen shugaban ƙasa sun fara tattaunawa tsakaninsu, da nufin gano bakin zaren kawo ƙarshen tashe-tashen hankula da ke gudana a ƙasar. Wannan arangamar ta biyo bayan yanke wa shugaban hukumar zaɓe na Gini da kuma mataimakinsa hukuncin shekara guda da koto ta yi, bisa laifin magudin zaɓe a zagayen farko na zaɓen shugaban ƙasa. Ranar 19 ga wannan wata na satumba, zagaye na biyu na zaɓen ya kamata ya gudana.

Cellou Dalein Diallo da ya zo na ɗaya a zagayen farko da kuma madugun 'yan adawan ƙasar wato Alpha Conde ne za su fafata tsakaninsu ,a zaɓen da ke zama irinsa na farko da ƙasar za ta gudanar bisa tsarin demokaraɗiya tun bayan da ta samun 'yancin kanta daga turawan mulkin mallaka na Faransa.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Halima Balaraba Abbas