1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasuwar Shugaban Kasar Guinea

Babangida JibrilDecember 23, 2008

Rasuwar Shugaban Kasar Guinea Lansana Conte

https://p.dw.com/p/GM8W
Marigayi Lansana ConteHoto: picture-alliance/dpa

Lansana Konte Dan shekaru 74 da haihuwa ya hau kan karagar mulki ne bayan wani juyin mulki da ya gudanar a shekarar 1984. Daga bisani dai ya mayar da kasar mai bin tafarkin mulkin Demokiradiyya,inda jam'iyar sa ce ke gudanar da harkokin mulki a tsawon wayan nan shekaru.

Kasar Guinea, ta kasance daya daga cikin kasashen yammacin Afrika dake fama da talauci,duk da albarkar ma'adinan karkashin kasa da Allah ya horewa kasar.

Sai dai kuma bayan mutuwar shugaban kasan keda wuya,yanzu haka rahotannin dake fitowa daga kasar na cewar,sojoji sun karbe ragamar shugabancin kasar.A wani jawabi da jagoran juyin mulkin yayi ta Radiyo Capt. Moussa David Camara,ya baiyana cewar wata majalisar tabbatar da Demokiradiya mai suna National Council for Democracy ta karbi ragamar gudanar da harkokin mulkin kasar.

Har ila yau jawabin da sojojin suka karanta ya baiyana dakatar da kundin tsarin mulkin kasar har sai abin da hali yayi.

A wani abu da ake ganin zai kasance rudani a kasar ta yammacin Afrika,yanzu haka dai shugaban majalisar Dokokin kasar Aboubakar Sompare ya bukaci kotun kolin kasar ta bayyana shi a matsayin shugaban wucin gadi, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar,kafin a gudanar da zabe a cikin kwanaki 60.

Tuni dai babban abokin adawar shugaban,wato Jean Marie Dore na jam'iyar cigaban kasar Giunea,ko Union of the progress of Guinea ya baiyana jimamin sa game da rasuwar shugaban.

Koda yake an fara samun martani daga kasashe da kungiyoyin kasa da kasa,amma bisa ga dukkan alamu kasashe da dama ba zasu amince da wannan juyin mulkin ba.

Yanzu dai a yayin da jama'ar kasar suke cikin rashin tabbas game da halin da kasar zata samu kanta a ciki,masu sharhi akan harkokin yau da kullum zasu zura ido domin ganin matakin da kasashen Duniya musanman Kasar faransa da tayiwa Guinein mulkin mallaka.