1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rattaba hannu a Yarjejeniyar sulhu da yan tawayen Tschadi

October 25, 2007
https://p.dw.com/p/C15h

Shugaba Idris Deby na kasar Tchadi tare da manyan kungiyoyin yan tawaye guda hudu,sun isa birnin Tripolin Libya domin rattaba hannu akan yarjejeniyar zaman lafiya,bayan tashe tashen hankula na baya bayan daya addabi wannan kasa dake tsakiyar Afrika.A garin Sirte ,dake gabashin Tripoli ne,akesaran bangarorin biyu zasu rattaba hannu a yarjejeniyar.shugaban kasar Sudan Omar El-Bashir na daga cikin masu sa idanu a wannan yarjejeniyarSakataren daya daga cikin kungiyoyin yan tawayen Tschadin,Abakar Tollimi,ya shaidar dacewa dukkannin shugabannin kungiyoyin adawan suna birnin Tripoli.