1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rawar kafofin yaɗa labarai a Tanzaniya

October 27, 2010

A ranar Lahadi al'ummar Tanzaniya za su je rumfunan zaɓe, domin kaɗa ƙuri'un su a zaɓukan ƙasar da ya ƙunshi jam'iyyun siyasa da dama

https://p.dw.com/p/Pqbb
Masu sa ido a zaɓe na EU a TanzaniyaHoto: EUEOM

Sai dai duk da cewar, sashen kafofin yaɗa labaran ƙasar ya sami bunƙasa sosai, amma alamu na nuni da cewar a halin da ake ciki, kafofin ba su kai matsayin bunƙasa tafarkin dimoƙraɗiyya mai ƙunshe da jam'iyyu masu yawa ba.

Tun lokacin da hukumomin Tanzaniya suka baiwa 'yan kasuwa masu zaman kansu damar shiga cikin harkokin yaɗa labarai a shekarun 1990 ne dai adadin kafofin ya riɓanya waɗanda ake da su, aƙalla a yankin tsakiyar ƙasar, wanda a yanzu ake samun taƙaitaccen 'yancin kafofin yaɗa labarai. Saboda haka, a yanayin zaɓen da ya haɗa jam'iyyun siyasa bakwai, a ƙasar da ke da fiye da jaridun 40 dake fitowa duk rana ko kuma mako mako, kana da tashoshin rediyo 50 da kuma na telebijin 30 za'a yi fatan kafofin za su kwatanta adalci wajen yaɗa manufofin jam'iyyun.

Sai dai kuma ba'a iya ganin hakan a yadda tashoshin ke yaɗa shirye shiryen su game da jam'iyyu daban daban da ke ƙasar. Wannan yanayi ya fi fitowa fili ne a tsibirin Zanzibar, wanda ke da ƙwarya ƙwaryar 'yanci a ta Tanzaniya. Yankin na da gidan jarida ɗaya tilo mallakar gwamnati, da tashar telebijin ɗaya, amma masu zaɓe a wurin ba za su yi iƙirarion samun bayanai kamar yadda dace ba.

Salim Sa'id Salim fitaccen ɗan jarida ne dake zaune a Zanzibar, wanda ya gudanar da binciken yadda kafofin yaɗa labarai ke tafiyar da sha'anin gangamin yaƙin neman zaɓe, amma sakamakon sa bai dace da ɗabi'u da kuma ƙa'idojin aikin jarida ba kamar yadda ya fadi:

"Kafofin yaɗa labaran gwamnatin Zanzibar ba sa bin ƙa'idojin aikin jarida, kuma idan an jawo hankalin su sai su ƙi. Misali Ali Muhammad Shein, ɗan takarar shugabancin Zanzibar na jam'iyyar CCM shi ne ya ke bayyana a shafin farko na jaridar gwamnati mai suna Zantibar Leo na tsawon wata guda. Sai ka sami hotuna ukku na 'yan takarar jam'iyyar CCM dake mulki tukuna kafin ka sami ɗaya na ɓangaren 'yan adawa."

Sai dai mutum zai ga banbanci idan ya ga yadda kafofin yaɗa labarai musamman na gwamnati ke bada rahotanni a tsakiyar ƙasar, inda suke ɗan kwatanta gaskiya hatta ga jam'iyyun adawa, ko da shike anan ma akwai dalilan da suka sa ake ganin kamar jam'iyyar CCM ce tafi mamaye tallace tallacen manufofin 'yan takara, kasancewar tana da ra'ayin kishin ƙasa, ga shi ta yi tsawon kimanin shekaru 50 tana mulki a ƙasar. Ko ta ina ka duba, kama daga manyan allunan, har ya zuwa shafukan jaridu da kuma tashoshin rediyo da telebijin, a zahiri za ka ga jam'iyyar CCM ce tayi kaka gida abinda a cewar Jenerali Ulimwengu, wanda shi kansa ɗan jarida ne da ke mallakar jaridar mako mako mai suna Raia Mwema ya ce ya yi amanna ga cancantar matsayin da jam'iyyar Chama cha Mapinduzi ko kuma CCM a taƙaice ta samu a kafofin yaɗa labaran Tanzania.

"Jam'iyyar Chama cha Mapinduzi tana da kuɗin daya zarta na sauran jam'iyyu, wanda shi ne dalilin daya sa ta sami damar yaɗa farfagandar ta. Alal misali idan ka dubi ɗaukacin manyan birane babu hotunan da za ka gani illa na ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyyar, da kuma na 'yan takarar majalisar dokoki kana dana ƙananan hukumomi na dai jam'iyyar."

A yayin da zaɓukan ƙasar Tanzaniya ke ƙara gabatowa, bincike ya nuna cewar shugaban ƙasar dake ci yanzu Jakaya Kikweti ya yiwa sauran 'yan takarar dake adawa shi zarra waɗanda suka haɗa da Farfesa Ibrahim Lipumba na jam'iyyar CUF da kuma Dakta Wilbroad Slaa na jam'iyyar CHADEMA ko dai a jaridu ko kuma a gidajen rediyo da telebijin ne.

Baki ɗaya dai, al'ummar Tanzania za ta je rumfunan zaɓe ba tare da kyakkyawar gudummowar kafofin yaɗa labarai ba ga tsarin dimoƙraɗiyya - mai jam'iyyu da dama. A hannu guda saboda jam'iyyun siyasaar ƙasar basu shiryawa hakan ba in banda jam'iyyar da ke mulki, yayin da a ɗaya hannun kuma su kansu kafofin yaɗa labaran ne alamu ke nunawa cewar, ba su da wani kyakkyaawan shiri na tinkarar tsarin dimoƙraɗiyya mai jam'iyyu masu yawa.

Mawallafa: Saleh Umar Saleh / Muhammad Khelef

Edita: Mohammad Nasiru Awal