1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rawar Rasha A Siyasar Duniya

February 14, 2006

Kasar Rasha ta sake wani sabon yunkuri domin a rika damawa da ita a siyasar duniya

https://p.dw.com/p/Bu1i
Vladmir Putin
Vladmir PutinHoto: picture-alliance / dpa/dpaweb

Wasu muhimman batutuwa guda biyu ne shugaba Putin da ministocinsa suka sa gaba. Da farko shawo kan shuagabannin Iran su kakkabe hannuwansu daga shirinsu na nukiliya, sannan na biyu fafutukar ganin an shigar da kungiyar Hamas a shawarwarin sulhu bayan gagarumar nasarar da ta samu a zaben Palasdinawa. Ita kuwa Iran ba ta yi wata-wata ba wajen soke ziyarar da aka shirya wakilanta zasu kai birnin Mosko. To sai dai kuma duk da haka akwai abubuwa da dama dake shaidar cewar a halin yanzu kasar Rasha ta fara samun kyakkyawan matsayin da ya dace da ita a siyasar duniya. A bangare guda tana da kyakkyawar dangantaka da kasashen Larabawa, wadanda ba su mika kai bori ya hau ga manufofin kasar Amurka ba, sannan a daya bangaren kuma tana da kakkarfar dangantakar tattalin arziki da kasar Iran. A baya ga haka martabar kasar Amurka ta zube a idanun duniya sakamakon yakin Iraki da kokarin kasar na shigar da manufofinta na demokradiyya a sauran kasashe na yankin gabas ta tsakiya ala-tilas. Ta la’akari da haka Rasha ka iya taka muhimmiyar rawa a matsayin mai shiga tsakani don sasantawa. To sai dai kuma gayyatar da tayi wa kungiyar Hamas ya zama tamkar wani kokari take yi ta janye daga sauran dangi. Amma abin lura a nan shi ne ita Rasha tana ba da la’akari ne ga ainifin maslaharta. Kasar ta dade tana fafutukar neman yin tasiri a siyasar duniya. Abin da take bukata shi ne ta daga matsayinta zuwa wata babbar daula ta duniya a daura da Amurka. Rasha na dari-dari da dangantakar Amurka da kasashen Georgiya da Azerbaijan kuma tana bakin kokarinta wajen kyautata dangantakarta da sauran kasashe makobta, musamman ma a yankin tsakiyar Asiya da kuma kasashen China da Indiya. A baya ga haka Rasha na ba da la’akari da maslahar kasuwanci. Kasar Iran, misali tana wa Rasha cinikin makamai, kazalika wasu kasashe na yankin. Gina tashoshin makamashin nukiliyar Iran na ma’anar kulla dangantakar ciniki da dogon lokaci kuma dubban masana kimiyya na kasar Rasha zasu ci gajiyar lamarin. A wannan bangaren Rasha na bin wasu manufofi ne guda biyu. Da farko manufar tattalin arziki sannan na biyu lafar da kurar rikici na siyasa. Domin kuwa duk da ba da la’akari da take yi ga maslaharta ta tattalin arziki kasar ta Rasha ba zata yi sha’awar ganin Iran ta mallaki makaman kare dangi ba. Amma duk da haka Rashan ba zata iyaatsi da Amurka a wannan halin da muke ciki yanzun ba tilas ne ta rika yin sara tana duban bakin gatarinta dangane da dangantaku na kasa da kasa da kuma alhakin dake kan fadar mulki ta Kremlin dangane da wadannan dangantaku.